Allah Ya Karbi Rayuwar Bello Maitama Bayan Fama Da Gajeriyar Jinya A Kano
- Tsohon ministan wasanni da matasa Dakta Bello Maitama Yusuf ya rasu a yau a Kano
- Marigayin wanda ya rike mukamai da dama a kasar ya rasu ne a gidansa da ke jihar Kano
- An bayyana marigayin, Sardaunan Dutse a matsayin mutum mai taimako wanda ya taba rayuwar mutane da dama
Jihar Jigawa - Tsohon ministan matasa da wasanni, Alhaji Dakta Bello Maitama Yusuf ya riga mu gidan gaskiya.
Dakta Bello ya rasu ne a gidansa da ke Kano a yau Juma'a 13 ga watan Oktoba bayan fama da jinya.
Yaushe marigayi Dakta Bello ya rasu a Kano?
Marigayin ya rike mukamai daban-daban a Najeriya da su ka hada da ministan kasuwanci da ministan cikin gida kuma tsohon Sanata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanata Bello Maitama ya rasu ne bayan ya sha fama da jinya na kankanin lokaci, kamar yadda Leadership Hausa ta tattaro.
Marigayin ya rasu ya na da shekaru 76 a duniya inda ya bar mata da yara 10 da su ka hada da maza biyar da mata biyar.
Wane ne marigayi Dakta Bello da ya rasu a Kano?
Bello ya kasance kwararren lauya ne wanda ya rike mukamin minista a Jamhuriya ta biyu.
Har ila yau, marigayin ya yi sanata a Jamhuriya ta hudu wanda ya ba da gudunmawa sosai a bangaren inganta rayuwar al'umma.
An sanar da lokacin sallar jana'izarshi wanda za a yi a fadar Sarkin Kano da zarar an idar da sallar Juma'a, cewar Leadership.
Wannan na zuwa ne bayan rasuwar wani dan majalisar Tarayya mai ci a jihar Sokoto.
Marigayi Abdulkadir Jelani Danbuga ya rasu bayan fama da jinya na kankanin lokaci wanda ya kwantar da shi a gadon asibiti.
Jelani ya rasu ne a Abuja a ranar Laraba 11 ga watan Oktoba wanda ya jawo dage zaman majalisar a ranar.
Shahararriyar jarumar Kannywood ta riga mu gidan gaskiya
A wani labarin, sharararriyar jarumar fina-finan Kannywood, Hajiya Binta Ola ta rasu bayan fama da jinya.
Marigayar ta rasu ne a gidanta dake Sabuwar Unguwa Kofar Kaura da ke cikin jihar Katsina.
Rahotanni sun tabbatar cewa, Ola ta gama shirya bikin Maulidi kenan a safiyar ranar inda ta rasu da dare kafin wayewar gari.
Asali: Legit.ng