Malamin Coci Ya Mutu a Wani Yanayi Mai Rikitarwa a Jihar Benuwai

Malamin Coci Ya Mutu a Wani Yanayi Mai Rikitarwa a Jihar Benuwai

  • Allah ya yi wa wani Babban Malami rasuwa a jihar Benuwai amma an samu ƙaulani kan yanayin da ya mutu a jihar Benuwai
  • Wasu na ganin tsawa ce ta faɗa masa ya mutu saboda lokacin ana ruwa yayin da wasu suka ce zame wa ya yi ya faɗa kan dutse
  • Hukumar 'yan sanda ta tabbatar da faruwar lamarin amma ta ce bincike ne kaɗai zai gano abin da ya kashe Faston

Jihar Benue - Rahoto ya nuna cewa ana zargin tsawa ta kashe babban malamin cocin St. Joseph Catholic da ke karamar hukumar Ukum ta jihar Benuwai, Rabaran Faustinus Gundu.

Rahoton Daily Trust ya tattaro cewa majiyoyi daga yankin da lamarin ya auku sun bada nau'i biyu na labarin yadda babban Malamin ya mutu.

Wani Malami ya mutu ana tsaka da ruwan sama.
Malamin Coci Ya Mutu a Wani Yanayi Mai Rikitarwa a Jihar Benuwai Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Ruɗanin da ya biyo bayan mutuwar Faston

Kara karanta wannan

Gwamnan APC a Arewa Ya Yi Fatali da Gargaɗin Gwamnatin Tinubu, Ya Haramta Muhimmin Abu 1 a Jiharsa

Nau'i na farko ya bayyana cewa babban limamin cocin wanda aka fi sani da "Albino" ya gamu da ajainsa ne sakamakon tsawar da ta faɗa masa sa'ilin da ake ruwan sama.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yayin da ɗaya sigar labarin ta nuna cewa Malamin ya yanke jiki ne ya faɗi kuma rai ya yi halinsa ranar Alhamis, 12 ga watan Oktoba.

Ganau sun yi iƙirarin cewa mamacin ya garzaya zuwa gidansa don ɗauko tawul jim kaɗan bayan da aka fara ruwan sama, kwatsam ya zame ya buga kansa a wani wuri mai ƙarfi.

An ce marigayi Gundu shi kadai ne a lokacin da lamarin ya faru kuma babu wanda zai kai masa ɗauki cikin gaggawa, haka ya ci gaba da zama a inda ya fadi ruwan sama na sauka.

Mazauna yankin sun ce lokacin da mutane suka ankara da abinda ya faru da Malamin, tuni rai ya yi halinsa.

Kara karanta wannan

'Dan Takarar Gwamnan PDP Ya Tsallake Rijiya da Baya Yayin da Aka Kai Masa Harin Kisa Sau 4 a Arewa

Yan sanda sun fara bincike

Jami’ar hulda da jama’a ta rundunar ‘yan sandan jihar Benuwai, SP Catherine Anene, ta tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin a garin Makurdi.

Sai dai kakakin 'yan sandan ba ta bada tabbacin sigar da Faston ya mutu ba, ko yanke jiki ya yi ko kuwa tsawa ce ta faɗa masa.

“Na samu rahoton amma mutane na zargin tsawa ce sanadi. Sai mun yi bincike kafin mu iya tabbatar da hakan.”

Wani mazaunin yankin ya shaida wa Legit Hausa cewa mutuwar Rabaran fada ta tada hankulan mutane kuma ga shi an rasa ainihin abin da ya yi ajalinsa.

"Ba Fasto bane, Rabaran Faza ne muna kiransa da Faza Orbute saboda Albino ne. shi, al'amrin ya faru ne a nan garin Zaki Biam, ƙaramar hukumar Ukum ta jihar Benue."
"Gaskiya lokacin da aka ganshi rai ya riga ya yi halinsa, kamar yadda kuka samu labari, mutuwar ta haddasa ruɗani to amma an fi bada ƙarfi kan tsawa ce ta yi ajalinsa."

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP Ya Bayyana Abu 1 da Zai Sanya Ya Yi Sulhu da Yan Bindiga a Jiharsa

- In ji mutumin mai suna, Bashir Galadima.

Ɗaliban Jami'ar Arewa da 'Yan Bindiga Suka Sace Sun Shaƙi Iskar 'Yanci

A wani rahoton na daban Daga karshe ɗaliban jami'ar jihar Nasarawa da aka yi garkuwa da su sun shaƙi iskar 'yanci ranar Alhamis, 12 ga watan Oktoba.

Dakarun sojin Bataliya ta 117 da ke Keffi ne suka samu nasarar ceto ɗaliban mata su huɗu bayan matsa wa yan bindigan lamba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262