Yan Bindiga Sun Halaka Wanda Ya Je Kai Kudin Fansa a Kaduna

Yan Bindiga Sun Halaka Wanda Ya Je Kai Kudin Fansa a Kaduna

  • Miyagun ƴan bindiga sun yi ajalin mutumin da ya je kai musu kuɗin fansa a ƙaramar hukumar Giwa ta jihar Kaduna
  • Ƴan bindigan bayan sun karɓi kuɗin fansan sun buƙaci mutumin da ya bi su zuwa cikin daji, inda shi kuma ya ƙi yarda
  • Hakan ya sanya suka buɗe masa wuta a bainar jama'a a a wurin da ya zama matattarar karɓar kuɗaɗen fansa a yankin

Jihar Kaduna - Wasu ƴan bindiga sun halaka wani mutum da ya je kai kuɗin fansa a jihar Kaduna.

Lamarin wanda ya auku a ƙauyen Kidandan da ke ƙaramar hukumar Giwa, ya sanya mazauna ƙauyen cikin firgici, cewar rahoton Daily Trust.

Yan bindiga sun halaka wanda ya je kai kuɗim fansa a Kaduna
Yan bindiga sun kashe wanda ya je kai musu kudin fansa a Kaduna Hoto: Channelstv.com
Asali: UGC

Mutumin wanda aka kashe mai suna Abdullahi Haruna mamba ne na ƴan agajin ƙungiyar Fitiyanul Islam. Ya dai bayar da kansa ne wajen kai kuɗin fansa domin a sako wani ɗan kauyen da ƴan bindigan suka sace.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Gindaya Sharaɗi Kafin Su Sako Ɗalibai Mata da Suka Sace a Jami'ar Arewa

Lamarin ya faru ne a ranar Laraba da misalin karfe 2:00 na rana a wani wuri da ake kira Sabo Layi a Kidandan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda lamarin ya auku

Wani ɗan banga da ya bukaci a sakaya sunansa ya tabbatar da aukuwar lamarin a ranar Alhamis, 12 gs watan Oktoban 2023.

Hakazalika, wani shugaban matasa a ƙauyen wanda ya bayyana sunansa a matsayin Jamil, ya ce ƴan bindigan sun buƙaci a biya su kuɗin fansa kan wani mutumin ƙauyen da suka sace.

Ya ce Abdullahi Haruna ya bayar da kansa domin kai wa ƴan bindigan kuɗin fansar.

Majiyar ya ce ƴan bindigan sun yi ƙoƙarin tilasta wa marigayin ya sauko daga babur ɗinsa bayan sun karɓi kuɗin fansa amma ya ƙi yarda inda ya ce musu kuɗin fansa kawai ya zo kawo wa.

"Sun harbe shi saboda ya ƙi bin su cikin daji. Hakan ya faru da rana da tsaka yayin da jama'a ke kallo a Sabon Layi." A cewar majiyar.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Kai Hari a Babbar Kasuwa a Jihar Arewa, Sun Halaka Bayin Allah

Ƙauyen na Sabon Layi shi ne cibiyar karɓar kuɗin fansa ga kusan dukkanin sace-sacen da ake yi a kusa da yankin.

Kokarin jin ta bakin jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sandan jihar, ASP Mansir Hassan, ya ci tura, saboda ba a samu layin wayarsa ba lokacin da aka kira shi.

Yan Bindiga Sun Halaka Mutane a Taraba

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu miyagun ƴan bindiga sun kai farmaki a wata kasuwa cikin dare a jihar Taraba.

Ƴan bindigan a yayin harin sun halaka mutum biyu tare da yin awon gaba da kayayyaki wanda darajarsu ta kai ta miliyoyin naira.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel