Matar Sarkin Bichi, Nasir Ado Bayero Ta Fada Tarkon Yan Damfara

Matar Sarkin Bichi, Nasir Ado Bayero Ta Fada Tarkon Yan Damfara

  • An damfari uwargidan Sarkin Bichi, Mai martaba Nasir Ado Bayero maƙudan kuɗaɗen da yawansu ya kai N20m
  • Hajiya Faridah Nasir Ado Bayero ta faɗa tarkon ƴan damfarar ne bayan an karɓi kuɗin da sunan sanya mata hannun jari a wani kamfani
  • Lamarin ya kai gaban kotun bayan hukumar EFCC ta gurfanar da wanda ake zargin domin a ƙwato mata haƙƙinta

Jihar Kano - Hajiya Faridah Nasir Ado Bayero uwargidan Sarkin Bichi, Mai martaba Nasir Ado Bayero, ta faɗa tarkon wani ɗan damfara a hannun wani wanda suke kasuwanci tare, cewar rahoton Aminiya.

Mai martaba Nasir Ado Bayero suruki ne a wajen tsohom shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.

An damfari uwargidan Sarkin Bichi
Mai martaba Sarkin Bichi, Nasir Ado Bayero Hoto: Masarautar Bichi
Asali: Facebook

Hukumar yaƙi da cin hanci da masu yi wa arzikin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) ta gurfanar da wanda ake zargin a gaban wata babbar kotun jihar Kano, a ƙarƙashin jagorancin mai shari'a Zuwaira Yusuf.

Kara karanta wannan

Muhimman Matakai 5 Da Gwamna Abba Ya Dauka Bayan Kotu Ta Kwace Nasararsa a Zabe

Ta wacce hanya aka damfare ta N20m?

Hukumar ta gurfanar da wanda ake zargin ne bisa tuhumar yin sama da faɗi da N20m.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wanda ake zargin Umar Bello Sadiq tare da kamfaninsa mai suna Marula Global Links Ltd, an gurfanar da su ne a gaban kotun bisa zargin karɓar N20m daga hannun uwargidan mai martaban da sunan sanya mata hannun jari a wani kasuwanci na ma'adanai.

Takardar shigar da ƙarar da aka gabatar a gaban kotun ta bayyana cewa bayan wanda ake zargin ya karɓi kuɗaɗen, ya karkatar da su ne domin amfanin kansa maimakon sanya a cikin kasuwancin.

Sai dai, wanda ake zargin ya musanta aikata laifin da ake tuhumarsa da shi a gaban kotun.

Lauyan wanda ake ƙara Shu'aibu Muazu ya buƙaci kotun da ta bayar da belin wanda yake karewa yayin da lauyan masu shigar ɗa ƙara, Sadiq Kurawa, ya buƙaci kotun da ta ɗage sauraron ƙarar.

Kara karanta wannan

Malamin Makaranta Ya Ɗebo Ruwan Dafa Kansa Bayan Ya Zane Ɗaliba Mace a Abuja

Kotu ta ba da beli

Mai Shari'a Zuwaira Yusuf bayan kammala sauraron bayanan lauyoyin, ta ba da belin Umar Bello a kan kuɗi N500,000 kan sharaɗin kawo mutum biyu da za su tsaya masa waɗanda dole su kasance ƴan uwansa na jini.

Alƙaliyar kotun ta kuma ɗage sauraron ƙarar har zuwa ranar 24, ga watan Nuwamban 2023 domin cigaba da shari'ar.

EFCC Ta Karbo Kudin Sata

A wani labarin kuma, hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa da masu yi wa arziƙin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) ta fara bincikar wasu manya ƙusoshi a ƙasar nan.

Hukumar ta bayyana cewa ta ƙwato N27bn da $19m da wasu tsiraru suka wawure daga asusun gwamnati.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng