Yadda Tinubu Ya Dauko Yaron Aminin Buhari, Ya ba Shi Muhimmin Mukami
- Aminu Maida zai jagoranci NCC bayan shugaban kasa ya kori Farfesa Umar Garba Danbatta wanda ya yi shekaru kusan takwas
- An nada shugabanni a NIPOST, NIGCOMSAT da Hukumar NCC da Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya kafa a shekarar 1992
- Dr. Maida ya yi digirin MEngr da PhD daga jami’o’in Ingila, ya yi aiki da kamfanoni da hukumomin gwamnati iri-iri
Abuja – Dr. Aminu Maida shi ne ya zama sabon shugaban hukumar nan ta NCC mai kula da duk wasu harkokin sadarwa a Najeriya.
Wata sanarwa da aka samu daga fadar shugaban Najeriya ya tabbatar da Aminu Maida ya canji Farfesa Umar Garba Danbatta.
Tun a Nuwamban shekarar 2015 ne Muhammadu Buhari ya nada Umar Garba Danbatta a NCC, aka tsawaita wa’adinsa a 2020.
Rahoton nan ya na kunshe da takaitaccen bayani ne game da rayuwa da aikin Maida.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wanene Aminu Maida?
1. Aminu Maida ya shafe sama da shekaru 15 ya na aikace-aikace da su ka shafi sadarwa da kasuwanci da fasaha.
2. Kafin wannan nadi, Malam Aminu Maida shi ne Babban Darektan fasaha da gudanarwa a bankin NIBSS na kasa.
3. Sabon shugaban na hukumar NCC ya taba zama babban jami’in fasaha (CTO) na kamfanin Arca Payments Network.
4. A shekarun baya ya zama Babban Manaja a kamfanin Cisco Systems UK a Birtaniya.
5. Idan aka shiga bangaren karatu, ya yi digirgir (Meng) a bangaren Injiniyancin daga jami’ar nan ta Imperial College a Landan.
6. Bayanai daga shafinsa na LinkedIn ya nuna Maida ya na da PhD daga jami’ar Bath a Landan a bangren Injiniyancin lantarki.
7. Da ya je Cambridge Judge Business School tsakanin 2018 da 2019 ya samu shaidar diflomar PGD a kan harkar kasuwanci.
Mahaifin Aminu Maida
8. Har ila yau CKNews ta ce mahaifinsa Marigayi Wada Maida, ya taba zama babban Sakataren yada labarai na Muhammadu Buhari.
'Danuwansa ya taya shi murna
Da mu ka tuntubi Na’im Bello a matsayinsa na ‘dan uwan sabon shugaban na NCC, ya shaida mana ana sa ran Aminu Maida zai ciri tuta a hukumar.
"Na yarda kwarewarsa domin amintacce ne, mai kokari kuma kwararren gaskiya.
Ya na da kwarewa daga bangarori dabam-dabam, wanda hakan ya sa ya san kan aiki."
- Na'im Bello
A wani rahoton da mu ka kawo a 2020, kun ji yadda Muhammadu Buhari ya rasa suruki, amini, da babban hadiminsa da na kusa da shi.
A shekarar nan Abba Kyari, Ismaila Isa Funtua da Wada Maida duk su ka rasu.
Asali: Legit.ng