Shugaba Buhari ya rasa Abba Kyari, Samaila Isa da Maida a shekarar 2020

Shugaba Buhari ya rasa Abba Kyari, Samaila Isa da Maida a shekarar 2020

Shekarar nan ta zo da labarai marasa dadi da-dama a Najeriya, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya na cikin wadanda su ka fi kowa shiga makoki a dalilin haka.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya rasa suruki kuma amini, da babban hadiminsa da wani tsohon abokinsa na tsawon shekara da shekaru a shekarar nan.

Mun kawo maku jerin wasu na-kusa da shugaban kasar da su ka mutu kamar yadda The Cable ta kawo su:

1. Abba Kyari

Abba Kyari shi ne wanda ya fara cikawa a cikin zagayen shugaban kasar. Babban hadimin fadar shugaban kasar ya mutu ne a sakamakon fama da ya yi da cutar COVID-19 a watan Afrilu.

Kyari bai da wata alaka ta jini da shugaban kasar, amma ya kasance babban mukarabbinsa.

2. Ismaila Isa Funtua

Kafin a gama makokin Abba Kyari, sai kuma Ismaila Isa Funtua ya rasu. Dattijon ya na cikin wadanda su ka ji mutuwar Kyari, Suruki ne wurin shugaban kasa, kuma amininsa.

KU KARANTA: Shahararrun mutanen da su ka mutu a 2020 a Najeriya

Shugaba Buhari ya rasa Abba Kyari, Sama Isa da Maida a shekarar 2020
'Danuwan Shugaba Buhari, Mamman Daura bai da lafiya
Asali: Twitter

Alhaji Samaila Isa kamar yadda aka fi saninsa da shi, ya dade a tafiyar Muhammadu Buhari.

3. Wada Maida

Alhaji Wada Maida ya rasu ne wata hudu bayan rasuwar Abba Kyari. Maida ya yi aiki da Buhari tun ya na shugaban kasa a mulkin soji, kuma ya na da mukami a gwamnatin nan.

Shugaba Buhari ya ji mutuwar tsohon ‘dan jaridar wanda ya taba zama sakataren yada labaransa.

Ana tsakiyar haka kuma sai aka ji cewa shararren kawun shugaban kasa Buhari watau Mamman Daura ya bar Najeriya, ana rade-radin dattijon bai da lafiya, ta-jitar da aka karyata tuni.

A wasu lokutan ana zargin wadannan Bayin Allah da rike madafan iko a kasar, sai dai babu wata kwakkwarar hujja da za ta iya gaskata wannan magana da ta bi bakin mutane rututu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel