Farashin Siminti: Yan Najeriya Sun Yi Martani Bayan Dangote Ya Musanta Yin Ragi
- Ƴan Najeriya sun koka sosai inda suka nuna matuƙar damuwarsu kan tsadar da siminti ya ke yi a Najeriya
- Hakan na zuwa ne bayan Dangote ya musanta ikirarin cewa ya rage farashin buhun siminti zuwa N2,400 da N2,700.
- Ƴan Najeriya sun yi kira ga gwamnati ta shiga tsakani kan farashin siminti saboda mawuyacin halin da tattalin arzikin da ake ciki a ƙasa
Wasu ƴan Najeriya sun bayyana ra'ayoyinsu kan wasan kwaikwayo da ake yi kan farashin buhun siminti a Najeriya.
Kwanan nan kamfanin simintin Dangote ya musanta rahotannin da ake yadawa a wasu kafafen yada labarai na yanar gizo (ba Legit.ng ba) dangane da batun yin tallace-tallace da kuma rage farashi zuwa N2,400 da N2,700.
Kamfanin ya fayyace cewa bai fara wani talla ko duba yiwuwar rage farashin kayansa ba kamar yadda aka yi iƙirari.
Kamfanin ya bayyana sanarwar da aka yaɗa a shafukan sada zumunta a ranar Lahadi, 8 ga Oktoba, 2023 a matsayin ƙarya ce tsagwaronta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar wacce aka yaɗa ta jaddada cewa kamfanin simintin Dangote zai sayar da simintinsa ga jama'a akan farashin masana'anta na naira 2,410 kacal kan kowane buhu.
Wannan dai ba shi ne karon farko da kamfanin ke musanta rahotannin rage farashin siminti ba.
Tun da farko ya yi watsi da iƙirarin cewa ya yi shirin rage farashin siminti da kaso 50.9% a ranar 1 ga Oktoba, 2023.
Ƴan Najeriya sun mayar da martani
Tuni dai ƴan Najeriya suka rika bayyana ra'ayoyinsu a shafukan sada zumunta na yanar gizo.
Ga wasu daga cikin martanin da aka yi a Facebook:
Pheel More Young-Azeez ya ce,
"Ya kamata su rage shi zuwa 1500 mu duka ƴan Najeriya ne."
Raheem Olatunde ya ce,
"Idan ya rage farashin yaya matsalar masu gidan haya, muna son gwamnatinmu ta shiga tsakani."
Umar Farouq ya rubuta:
"Rashin ragewan shi bazai hana siya bah!"
Usama Abdullahi Skf ya rubuta:
"Allah shi horewa kowa abin saya"
Shamsuddeen Baso Sharada ya rubuta:
"Insha Allah sai ka dawo na ɗari biyu a masu arziƙin Najeriya, mara adalci."
Matatar Dangote Ta Fadi Lokacin Fara Aiki
A wani labarin na daban kuma, matatar man fetur ɗin Dangote ta bayyana ainihin lokacin da za ta fara tace ɗanyen mai.
Matatar ta bayyana cewa a cikin watan Oktoban 2023 za ta fara aikin tace ɗanyen man fetur domin rage dogaro da shigo da shi da ake yi daga ƙasar waje.
Asali: Legit.ng