Yan Bindiga Sun Halaka Basarake, Sun Yi Awon Gaba da Mutane da Yawa a Niger

Yan Bindiga Sun Halaka Basarake, Sun Yi Awon Gaba da Mutane da Yawa a Niger

  • Yan bindiga sun yi ajalin Basarake, sun tattara jama'a sun yi awon gaba da su a ƙauyukan jihar Neja ranar Talata da daddare
  • Rahotanani daga mazauna yankin sun nuna cewa maharan sun haɗa harda mata sun yi garkuwa da su, sun sace dabbobi
  • Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Neja ya tabbatar da kai sabon harin amma ya ce har yanzun bai samu cikakken rahoto ba

Jihar Niger - Miyagun 'yan bindiga sun kashe Magajin Garin Zazzaga da ke ƙaramar hukumar Munya a jihar Neja, Mallam Usman Sarki.

Rahoton Daily Trust ya tattaro cewa tsagerun 'yan bindigan sun kai farmaki ƙauyen Zazzaga da wasu ƙauyuka da ke maƙwaftaka da shi ranar Talata da daddare.

Yan bindiga sun kai sabon hari a jihar Neja.
Yan Bindiga Sun Halaka Basarake, Sun Yi Awon Gaba da Mutane da Yawa a Niger Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Yadda maharan suka yi ta'asa a ƙauyuka

Wasu majiyoyi sun bayyana cewa 'yan ta'addan sun yi garkuwa da mutane masu ɗumbin yawa da har yanzun ba a gama tantance adadinsu ba yayin harin.

Kara karanta wannan

Babban Hafsan Tsaron Najeriya Ya Dira Jihar Arewa, Ya Aike da Kakkausan Saƙo Ga Yan Ta'adda, Ya Ba Su Zaɓi 2

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta saboda dalilan tsaro, ta ce:

"Sun shigo da daddare ranar Talata, suka bindige Magajin gari, Mallam Usman Sarki, har lahira kana suka yi awon gaba da wasu mutane masu yawa."
"A yanzu ba zan iya faɗa muku adadin mutanen da suka ɗauka ba, bayan haka sun sace dabbobin da muka mallaka."

A rahoton Premium Times, wata majiyar ta daban ta ce:

"Ban san adadin mutanen da aka sace daga wasu kauyuka ba saboda an kai harin ne cikin dare. Don haka kowa ya gudu zuwa daji amma sun yi garkuwa da mutane da yawa."
"A kauyen Kutara da ke makwabtaka da Zazzaga inda na fito, an yi garkuwa da mutane bakwai da suka hada da mata yayin harin, adadin da na sani kenan. Sun kuma sace mana shanu."

Kara karanta wannan

'Yan Sanda Sun Ragargaji Yan Bindiga, Sun Ceto Sama da Mutum 170 da Aka Sace a Jihar Arewa

Shin jami'an tsaro sun samu rahoton abinda ya faru?

Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Neja, DSP Wasiu Abiodun, ya tabbatar da faruwar harin amma ya ce har yanzu bai samu cikakken bayani ba.

Katsina: Gwamnonin Arewa Ta Yamma Sun Hadu Don Magance Matsalar Tsaro da Noma

A wani rahoton na daban kuma Gwamnoni 6 sun yi zama na musamman a Katsina kan matsalar tsaro da harkar noma.

Gwamnonin sun ce dukkansu sun amince za su yi aiki tare don inganta harkar noma ta hanyar dabarun zamani da kuma samar da kayayyaki da kasuwanni.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262