Shugaban Jam'iyyar PDP A Jihar Osun Ya Riga Mu Gidan Gaskiya Jim Kadan Bayan Barin Ofis
- Ana cikin jimami yayin da mutuwa áta riski shugaban jam'iyyar PDP a karamar hukumar Ede ta Arewa a jihar Osun
- Marigayin, Alhaji Jimoh Oyekanmi ya rasu a daren jiya Talata 10 ga watan Oktoba bayan barin ofis
- Jam'iyyar yayin sanar da mutuwar, ta nuna kaduwarta tare da sanya makoki har na tsawon kwanaki uku da dakatar da dukkan ayyukan jam'iyya
Jihar Osun - Jam'iyyar PDP a jihar Osun ta sanar da mutuwar shugaban jam'iyyar na karamar hukumar Ede ta Arewa, Mista Jimoh Oyekanmi.
Shugaban jam'iyyar a jihar, Sunday Bisi ya ce mutuwar Oyekanmi ta zo a bazata bayan ya bar ofis a yammacin jiya Talata 10 ga watan Oktoba.
Yaushe shugaban PDP ya rasu a Osun?
Bisi ya nuna kaduwarshi kan mutuwar Oyekanmi inda ya ce mutum ne mai aiki tukuru wanda ba ya gajiya, cewar Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yayin da ya ke jajantawa iyalan mamacin da dukacin al'ummar jihar, ya ce jam'iyyar da dakatar da duk wasu ayyuka na siyasa, National Daily ta tattaro.
Ya ce an saka kwanaki uku na zaman makoki a jihar don yi masa addu'o'in dace wa a gaba, City Mirror ta tattaro.
Wane mataki PDP ta dauka a Osun don jajantawa?
Sanarwar ta ce:
"Jam'iyar PDP a jihar Osun ta kadu da mutuwar shugaban jam'iyyar a karamar hukumar Ede ta Arewa.
"Mutuwar abin takaici ne ganin yadda ta zo ba zato a daren jiya Talata 10 ga watan Oktoba.
"Yayin da mu ke jimamin mutuwar Alhaji Oyekanmi, mun dakatar da dukkan ayyukan jam'iyya na kwanaki uku kuma a saukar da tutocin jam'iyyar a ko ina."
Jam'iyyar ta mika sakon ta'aziya ga iyalan marigayin da jam'iyyar PDP da kuma daukacin al'ummar jihar Osun.
Dan majalisar Tarayya a Sokoro ya rasu
A wani labarin, dan majalisa mai wakiltar mazabar Sabon Birni a jihar Sokoro Abdulkadir Jelani Danbuga ya riga mu gidan gaskiya.
Dan majalisar wanda ya fito daga jam'iyyar APC ya rasu ne a daren Laraba 11 ga watan Oktoba bayan gajeriyar jinya da ta kwantar da shi a asibiti.
Asali: Legit.ng