Jami'ar CSU: Babu Hujja Cewa Tinubu Ya Kirkiri Takardan Jabu, In Ji BBC
- Tawagar Tantance Bayanai ta Gidan Watsa Labarai na Birtaniya, BBC, ta tabbatar da nagartar takardar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ba wa INEC
- Tawagar ta BBC ta ce babu hujja cewa takardar ta CSU da Tinubu ya bai wa INEC kirkirar ta ya yi
- A cewar binciken na BBC, takardar ta shugaban kasa ta yi kamanceceniya da wasu shaidan difloma uku na CSU da aka bai wa Atiku Abubakar
Birtaniya - Tawagar tantance bayanai na gaskiya na Kafar Watsa Labarai na Birtaniya (BBC) ta wallafa rahoto kan batun takardan shaidar karatun Shugaba Bola Tinubu na Najeriya.
Wadanda suka rubuta rahoton mai taken: 'Bola Tinubu diploma: No evidence Nigeria’s president forged college record’ sun cimma matsayar cewa Shugaba Tinubu bai kirkiri takardan karatu na bogi ba.
Cikakken Jerin Takardun Karatun da Tinubu, Atiku, Peter Obi, Kwankwaso Suka Ba INEC Kafin Zaben 2023
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Zargin cewa Shugaba Tinubu ya kirkiri takardan karatu na karya ya bazu tamkar wutar daji a kafafen sada zumunta bayan Jami'ar Jihar Chicago (CSU) ta saki bayanan karatun shugaban kasar.
Sakin takardun karatun na Tinubu ya zama babban lamari a karar da Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP ya shigar na kallubalantar cancantar takarar shugaban kasar.
BBC ta cimma matsayanta ne bayan ta tuntubi CSU da hadimin Atiku don neman bayanai kan takardun da jami'ar ta saki game da shaidar difilomar Tinubu.
Dakaci karin bayani ...
Asali: Legit.ng