"Ku Tuba Ko Ku Zarce Lahira" CDS Ya Aike da Sako Ga Yan Ta'adda a Najeriya
- Babban hafsan tsaro na ƙasa (CDS) ya kai ziyarar aiki ga rundunar Operation Haɗin Kai, ya aike da sako ga yan ta'adda
- Janar Christopher Musa ya roƙi 'yan Najeriya su ci gaba da taimaka wa hukumomin tsaro da bayanan sirri don kawo karshen matsalar tsaro
- Ya kuma yaba wa gwamna Zulum na jihar Borno bisa goyon bayan da yake baiwa sojoji da sauran jami'an tsaro
Jihar Borno - Babban hafsan hafsoshin tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su hada kai wajen yaki da rashin tsaro ta hanyar bai wa jami'an tsaro sahihan bayanan sirri.
CDS ya yi wannan kira ne yayin zantawa da 'yan jarida a jihar Borno sa'ilin da ya kai ziyarar aiki ga rundunar Operation Haɗin Kai ranar Talata, Daily Trust ta rahoto.
Ya kuma gargaɗi 'yan ta'addan kungiyar Boko Haram da sauran makamantansu da suka hana zaman lafiya a Arewa maso Gabas su miƙa wuya ko a raba su da duniya ta kowane hali.
Ya ce:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Idan kuka ga wani abu, ku zo su gaya mana, ku yi hakan da haɗin kai domin mu samu nasara a yakin da ake da rashin tsaro. Yaki da rashin tsaro ba alhakin sojoji kadai ba ne."
Ya ce dakarun soji karkashin jagorancinsa da taimakon Allah, shugaban kasa Bola Tinubu da masu ruwa da tsaki, a shirye suke su kawo karshen ta’addanci, garkuwa da mutane da sauran laifuka a kasar nan.
Babban hafsan tsaron ya bai wa yan ta'adda zaɓi 2
"Bayanin da na karɓa daga kwamanda, Manjo Janar Gold Chibusi, da kwamandan runduna ta 7, Manjo Janar Peter Malla, na gamsu da nasarorin da aka samu wajen murƙushe Boko Haram.
"Duk da haka, ina so in yi kira ga sojoji da kada su yi ƙasa a guiwa, su ci gaba da jajircewa da matsa ƙaimu har sai sun kawo karshen matsalar gaba ɗaya."
“Ina kuma ƙara jaddada kiranmu ga ragowar ‘yan ta’adda, masu garkuwa da sauransu da su mika wuya ko kuma a kashe su, domin mun kuduri aniyar dawo da zaman lafiya a kowane lungu da sako na kasar nan.”
- Janar Christopher Musa.
CDS ya ziyarci gwamna Zulum
A gidan gwamnatin jihar Borno yayin da ya kai ziyarar ban girma ga Gwamna Zulum, CDS ya baiwa al'ummar jihar tabbacin samun zaman lafiya, Vanguard ta ruwaito.
Ya kuma yaba wa Gwamna Zulum bisa irin goyon bayan da yake bai wa sojoji, wanda ya sa dubban ‘yan Boko Haram suka mika wuya a karkashin ayyukan sa.
A nasa jawabin, Farfesa Zulum, ya bayyana CDS a matsayin jami’i mai himma, kwazo da tsoron Allah, ya kuma yi alkawarin ci gaba da tallafa wa sojoji da sauran hukumomin tsaro a jihar.
Yan Sanda Sun Ceto Mutane 171 da Aka Yi Garkuwa Da Su a Jihar Katsina
A wani rahoton kuma Dakarun rundunar 'yan sandan jihar Katsina sun sheƙe yan bindiga huɗu, sun ceto mutane sama da 170 da aka yi garkuwa da su.
Kakakin rundunar, ASP Abubakar Aliyu, ya ce jami'ai sun kuma kwato muggan makamai da dabbobi da babura da aka sace.
Asali: Legit.ng