Kano: Muhimman Abubuwa 5 Da Gwamna Abba Ya Yi Bayan Rashin Nasara a Kotu
Jihar Kano - Bayan kotun zaɓe ta soke zaɓensa, gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) ya bayyana hukuncin da cewa ba komai bane illa koma baya na wucin gadi.
Gwamnan ya kuma bayyana cewa yana da tabbacin babu shakka cewa hukuncin yana cike da kurakurai da rashin yin amfani da doka yadda ya dace, domin haka ba zai yi tasiri ba a kotun ɗaukaka ƙara da kotun ƙoli, cewar rahoton Daily Trust.
Gwamnan ya kuma bayyana cewa ba zai yi ƙasa a gwiwa ba wajen cimma abubuwan da shi da jam'iyyarsa suka yi wa al'ummar jihar Kano alƙawari.
Ga abubuwa biyar da gwamnan jihar Kano, Abba Yusuf, ya yi tun bayan da kotun ta yanke hukunci.
1. Dawo da aikin tituna a ƙananan hukumomi 44
Gwamnan ya umarci ƴan kwangilar da ke tafiyar da ayyukan tituna masu tsawon kilomita biyar a dauƙacin ƙananan hukumomin jihar 44 da su koma bakin aiki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso ne ya fara aikin titunan masu tsawon kilomita biyar amma an yi watsi da su tsawon shekaru takwas.
2. Naɗin ƙarin mataimaka
Kwanaki kaɗan bayan yanke hukuncin kotun, gwamna Yusuf ya sanar da sabbin naɗe-naɗen hadimai 94 da gwamnatin ta kare a matsayin wani mataki da ya dace da alƙawuran shigar da matasa cikin harkokin mulki da kuma haɗa hannu da su wajen sauke nauyin da aka dora musu.
A mako biyu da suka gabata, gwamnan ya kuma sanar da naɗin ƙarin mataimaka 116 da suka haɗa da manyan mataimaka na musamman (SSA) 63, mataimaka na musamman (SA) 41 da mataimaka na musamman (PA) 12.
3. Kyautar kuɗi ga marasa lafiya
Gwamna Yusuf ya kuma baiwa majinyata a babban asibitin Sir Sanusi kuɗi N20,000 kowannensu. Gwamnan ya bayar da kuɗaɗen ne bayan ya kai ziyarar bazata a asibitin.
Ya kuma baiwa wata ma'aikaciyar wucin gadi mai suna Khadija Adam aiki na dindindin saboda ƙwazonta a lokacin ziyarar bazata da ya kai asibitin.
Gwamnan ya kuma bayar da umarnin a gaggauta gyara asibitin wanda ya lalace.
4. Amincewa da N700m ga ɗaliban BUK
A watan Agustan 2023, majalisar zartaswar jihar Kano ta amince da fitar da N700m domin biyan kuɗin makaranta ga ɗalibai ƴan asalin jihar 7,000 da ke karatu a jami'ar Bayero da ke Kano (BUK).
Gwamnan ya ɗauki wannan matakin ne biyo bayan ƙarin kuɗin makaranta da jami'ar ta yi.
5. Rage kaso 50% na kuɗin makaranta
A watan Agustan 2023, gwamnan ya ba da sanarwar rage kaso 50% na kuɗaɗen makaranta ga ɗaliban da ke karatu a manyan makarantun jihar.
Wannan mataki da gwamnan ya dauka ya samu yabo daga iyaye da masu faɗa a ji a jihar.
Gwamna Abba Ya Ba Matashi Aiki
A wani labarin kuma, gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ba matashin da ya dawo da dala miliyan 16 da ya tsinta a lokacin aikin Hajji, kyauta mai tsoka.
Gwamnan ya ɗauki matashin aiki sannan ya ba shi kyautar naira miliyan ɗaya da kujerar zuwa aikin Hajji.
Asali: Legit.ng