Kotu Ta Daure Babban Janar Din Soja Bisa Laifin Satar Kudade
- Kotun sojojin Najeriya ta musamman ta zartar da hukunci kan tsohon shugaban kamfanin NAPL da ake tuhuma da laifin sata
- Kotun mai alƙalai takwas ta samu Manjo Janar Umar Mohammed da laifin yin sama da faɗi da kuɗaɗen kamfanin
- Kotun ta tura shi gidan gyaran hali tare da umartarsa ya dawo da wasu kuɗaɗe na kamfanin da ya sace
FCT, Abuja - Kotun Sojan Najeriya ta musamman da ke zamanta a Abuja, ta samu wani tsohon Manajan Daraktan kamfanin kula da kadarorin rundunar sojin ƙasa ta Najeriya (NAPL), Manjo Janar Umar Mohammed, da laifin satar kuɗaɗen kamfanin.
Tun da farko dai rundunar sojin ta gurfanar da Mohammed ne a kan tuhume-tuhume 18 da suka haɗa da amfami da takardun jabu, almubazzaranci da kuɗaɗe, haɗa baki domin aikata laifi da sauransu.
Sai dai, wanda ake zargin a baya ya musanta aikata laifukan da ake tuhumarsa da su.
Daily Trust ta ce a cigaba da zaman kotun na ranar Talata, 10 ga watan Oktoban 2023, kotun mai alƙalai takwas ƙarƙashin jagorancin Manjo Janar James Myam, ya bayyana cewa an samu babban jami'in sojan da laifuka 14 cikin 18.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Alƙalin ya bayyana cewa lauyoyin masu gabatar da ƙara sun gabatar da shaidu 24, yayin da wanda ake ƙara ya kira shaidu biyu.
Wane hukunci kotun ta yanke?
Bayan haka, a hukuncin da ya yanke, ya bayar da umarnin a ɗaure babban jami'in shekaru biyar kan kowanne daga cikin wasu laifukan da ake tuhumarsa da su, yayin da wasu kuma ke da hukuncin ɗaurin shekara bakwai da shekara biyu.
Yayin da yake bayyana cewa hukuncin zai gudana ne a lokaci guda, kotun ta kuma umarce shi da ya mayar da wasu kuɗaɗe a asusun NAPL.
Dubu Ta Cika: An Kama Wata Mata Ɗauke da Kwalayen Kayan Laifi Sama da 50 a Filin Jirgin Sama a Jihar Kano
Myam ya bayyana cewa hukuncin da aka yanke masa sai masu ikon tabbatarwa sun amince da shi kafin ya fara aiki.
Kafin a yanke masa hukunci, Mohammed ya kasance a wurin da ake tsare sojojin Najeriya a Mogadishu, Abuja inda ya shafe sama da shekaru 2.
Rundunar Tsaro Ta Bukaci Hadin Kan Yan Najeriya
A wani labarin kuma, rundunar tsaro ta Najeriya ta buƙaci haɗin kan ƴan Najeriya domin magance matsalar tsaron da ta addabi ƙasa.
Rundunar ta bayyana cewa ita kaɗai ba za ta iya magance matsalar tsaron da ta ƙi ta ƙi cinyewa ba a ƙasar nan.
Asali: Legit.ng