"Muna Tare da Palastine" 'Yan Shiga Sun Fito Tattakin Goyon Baya a Abuja

"Muna Tare da Palastine" 'Yan Shiga Sun Fito Tattakin Goyon Baya a Abuja

  • Wasu gungun mabiya aƙidar shi'a a Najeriya sun fito tattakin nuna goyon baya ga Falasɗinawa bayan sabon yaƙin da ya ɓarke
  • Sheikh Sidi Munir Sokoto, ya ce ƙungiyar Shi'a IMN karkashin Sheikh Zakzaky ra saba gudanar da zanga-zangar goyon bayan Falasɗinu
  • Wannan na zuwa ne awanni bayan samamen da mayakan Falasɗinawa suka kai na ramuwar gayya kan Isra'ila

FCT Abuja - 'Yan shi'a ƙarƙashin kungiyar Islamic Movement in Nigeria (IMN) sun bayyana goyon baya ga Falasdinawa biyo bayan sake ɓarkewar rikici tsakanin Isra'ila da Falasdinu.

Ana alaƙanta sabon yaƙin da ya ɓarke da farmakin da aka kai Masallaci Al-Aqsa da kuma sansanin 'yan gudun hijira da ke Gaza.

Yan shi'a sun yi zanga-zanga a Abuja.
"Muna Tare da Palastine" 'Yan Shiga Sun Fito Tattakin Goyon Baya a Abuja Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Kamar yadda Daily Trust ta tattaro, daga ranar Asabar zuwa yanzun ɓangarorin biyu watau Isra'ila da Falasɗinawa sun yi asarar rayuka aƙalla 1,000.

Kara karanta wannan

Dubu Ta Cika: An Kama Wata Mata Ɗauke da Kwalayen Kayan Laifi Sama da 50 a Filin Jirgin Sama a Jihar Kano

An ce Falasdinu ta rasa mutane 421 yayin da mutanen Isra'ila sama da 700 suka mutu. An kuma sanya adadin wadanda suka jikkata da 2, 220 da 2, 156 bi da bi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rundunar mayaƙan Hamas Al-Qassam Brigades, watau Falasdinawa da ke mulkin zirin Gaza, ta ce ta kai samamen ramuwar gayya a ranar Asabar din da ta gabata.

A cewarta, ta kaddamar da farmakin ne a matsayin maida martani ga "ci gaba da cin zarafin" da Isra'ila da gwamnatin mamaya su ke yi wa Falasdinawa.

'Yan shi'a sun fita zanga-zangar nuna goyon baya

Tawagar mabiya aƙidar shi'a sun fara tattakin goyon bayan Falasɗinawa da misalin ƙarfe 4:00 na yammacin ranar Litinin.

Sun gudanar da tattakin daga Banex Plaza kuma suka ƙarkare a fitilun kan titin Ahmadu Bello Way da ke cikin birnin tarayya Abuja, BBC Hausa ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Soyayyar Damfara: Baturiya Ta Bayyana Yadda Dan Yahoo Yahoo Ya Damfare Ta Kudi Har N122m

A wata sanarwa, Sheikh Sidi Munir Sokoto, na ƙungiyar 'yan shi'a ya ce:

"Mun tsinci kanmu a wani yanayi da ba mai guje masa, ya zama kaddara. Duk abin da ya shafi mutum ɗaya kai tsaye yana shafar duka a kaikaice."
“Sama da shekaru 30, ƙungiyar shi'a karkashin Shaikh Ibraheem Zakzaky, tana tsara shirye-shirye da zanga-zangar nuna goyon baya ga al’ummar Falasɗinu da ake zalunta."
“Duba da abubuwan da suke faruwa, muna kira ga dukkan al’ummar Nijeriya da su karya shirun da suka yi na kurma, su ɗaga muryar goyon bayan Falasdinawa da ake zalunta."

NDLEA Ta Kama Wata Mata da Tulin Haramtattun Kwayoyi a Filin Jirgin Kano

A wani rahoton kuma Jami'an hukumar NDLEA sun cafke wata mai suna Bilkisu ɗauke da ƙunshin holar iblis sama da 50 a filin jirgin Aminu Kano.

A wata sanarwa da hukumar ta fitar, ta ce an kama matar ne yayin da take shirin kama jirgi zuwa ƙasa mai tsarki ranar Talata.

Kara karanta wannan

"Akwai Babban Abin Damuwa" INEC Ta Bayyana Abinda Ta Hango Zai Kawo Cikas a Zaɓen Gwamnoni 3

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262