Shugaba Tinubu Ya Yi Sabbin Nade-Naden Mukamai a Gwamnatinsa

Shugaba Tinubu Ya Yi Sabbin Nade-Naden Mukamai a Gwamnatinsa

  • Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi sabbin naɗe-naɗen masu taimaka masa na musamman guda biyar
  • Sabbin naɗe-naɗen na shugaban ƙasa Tinubu dai za su yi aiki ne a ƙarƙashin tawagar ofishin yaɗa labarai na shugaban ƙasa
  • Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Ajuri Ngelale, shi ne ya tabbatar da naɗin da aka yi musu a cikin wata sanarw ranar Litinin, 9 ga watan Oktoba

FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi naɗin sabbin hadimai da za su yi aiki a gwamnatinsa.

Shugaban ƙasar ya naɗa sabbin hadimai guda biyar da za su yi aiki a matsayin mataimakansa na musamman a ofishin yaɗa labarai da wayar da kan jama'a.

Shugaba Tinubu ya yi sabbin nade-nade
Shugaba Tinubu ya yi sabbin nade-nade guda biyar Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasan, Ajuri Ngelale, ya fitar a ranar Litinin, 9 ga watan Oktoban 2023.

Kara karanta wannan

"Akwai Babban Abin Damuwa" INEC Ta Bayyana Abinda Ta Hango Zai Kawo Cikas a Zaɓen Gwamnoni 3

Jerin sabbin naɗe-naɗen Shugaba Tinubu

Ga jerinsu kamar haka:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1. Mista Fela Durotoye (Babban mataimaki na musamman ga shugaban ƙasa - (Ƙimar ƙasa da adalci ga jama'a)

2. Mista Fredrick Nwabufo (Babban mataimaki na musamman ga shugaban ƙasa - Tattaunawa da jama'a)

3. Misis Linda Nwabuwa Akhigbe (Babbar mataimakiya ta musamman ga shugaban ƙasa - Dabarun sadarwa)

4. Malam Aliyu Audu (mataimaki na musamman ga shugaban ƙasa - Harkokin jama'a).

5. Mista Francis Adah Abah (Mataimaki na musamman ga shugaban ƙasa - Ayyuka na musamman)

Shugaba Tinubu ya ƙara amincewa da naɗa Misis Linda Nwabuwa Akhigbe a matsayin mai baiwa shugaban hukumar ECOWAS shawara kan harkokin sadarwa.

Shugaban ƙasar ya buƙaci masu sabbin muƙaman da waɗanda ke aiki a sashin yada labarai da wayar da kan jama’a da su tabbatar da kyawawan ƙa’idoji na mutunci a cikin harkokinsu da daukacin al’umma yayin da suke cigaba da ƙoƙarin da shugaban ƙasa ke yi na sabunta fata ga ƴan Najeriya a cikin tsarin sake fasalin tattalin arziki da haɗin kan al'umma da ya dace da bukatun kowa, ba tare da la'akari da kowane bambanci ba.

Kara karanta wannan

Jerin Gwamnonin Da Suka Nada Hadimai Tsakanin 100 Zuwa Sama Da 400 Tun Bayan Hawa Mulki

Gwamnatin Bauchi Za Ta Dalibai Mata Tallafi

A wani labarin kuma, gwamnatin jihar Bauchi za ta riƙa biyan ɗalibai mata na makarantun sakandire tallafin kuɗaɗe.

Gwamnatin za ta riƙa biyan kuɗaɗen ne domin ƙarfafa gwiwar yara mata su riƙa zuwa makaranta musamman waɗanda iyayensu ba su da hali sosai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng