Soyayyar Damfara: Baturiya Ta Bayyana Yadda Ta Rasa N122m a Hannun Dan Yahoo

Soyayyar Damfara: Baturiya Ta Bayyana Yadda Ta Rasa N122m a Hannun Dan Yahoo

  • Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa (EFCC) ta gurfanar da wani matashi Wilson Daphey a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja
  • An gurfanar da Daphey a gaban kotun ne bisa tuhume-tuhume tara da suka haɗa da samun kudi ta hanyar ƙarya da kuma karkatar da kuɗaɗe
  • Matashin ɗan Najeriya da ake zargin ya yi ƙarya tare da karbar kusan fam 130,000 daga hannun wata baturiya Ms Petra Goschenhofer

FCT, Abuja - Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ƙasa (EFCC) a ranar Juma'a, 6 ga Oktoba, 2023, ta cigaba da shari’ar Wilson Daphey, wanda kuma aka sani da Jeffrey Guiseppe.

A cewar wata sanarwa da hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta wallafa a shafukan sada zumunta, an gurfanar da Daphey a gaban mai shari’a Mobolaji Olajuwon na babbar kotun tarayya da ke Abuja.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Kotu Ta Yanke Hukunci Kan Dan Sandan Da Ya Halaka Lauya a Legas

Baturiya ta fada hannun dan Yahoo Yahoo
Dan Yahoo Yahoo ya damfari wata Baturiya N122m Hoto: Economic and Financial Crimes Commission, Daniel Ayantoye
Asali: Facebook

Ana zargin Daphey da yin ƙarya tare da karbar kudi har Fam 130,000 (kimanin N122m) daga hannun wata Baturiya ƴar ƙasar Jamus, Ms Petra Goschenhofer.

Ya aikata wannan laifin ne tare da taimakon abokansa: Ifeanyi Enuma, Evans Nnamdi Aguh, Christopher Chinedu Ajufo, da Ojinanaka Kingsley Chukwuma, wadanda dukkaninsu yanzu sun tsere.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta yaya matashin ya damfare ta?

A cigaba da shari'ar a makon da ya gabata, Goschenhofer ta bayyana yadda ta ke "mu'amala da wani bature wanda daga baya ya rikiɗe ya zama baƙar fata ɗan Najeriya."

A kalamanta:

"Bayan wani lokaci, sai ya ce min yana sona, na ce masa ina da aure da ƴaƴa, cewa soyayya ba ta yiwuwa a tsakaninmu amma bayan wani lokaci, sai na lura yana kyautata min kuma a lokacin ina cikin wani hali, aurena ya shiga matsala, na shiga damuwa, sannan ɗa na yana cikin yanayi mara kyau."

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: An Maka Akpabio Da Wasu Sanatoci Kara a Gaban Kotu, Bayanai Su Fito

"A hankali na fara soyayya da shi, kuma ba da dadewa ba, ya fara neman na tura masa kuɗi, na tura masa kuɗin ta hanyar Western Union. Dukkanin kuɗaɗen da na tura masa sun kai aka fam 13,000."

Legit.ng ta fahimci cewa, Mai shari'a Olajuwon ya ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar Talata,10 ga watan Oktoban 2023, domin jin bayanan wanda ake tuhuma.

Kotu Ta Yankewa Dan Sanda Vandi Hukunci

A wani labarin kuma, wata babbar kotun jihar Legas ts yanke hukunci kan shari'ar wani jami'in ɗan sanda mai suna Drambi Vandi, wanda ya halaka wata lauya.

Kotun ta zartar da hukuncin kisa ta hanyar rataya kan ɗan sandan bayan ta same shi da laifin halaka Bolanle Raheem.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng