Yan Bindiga Sun Sace Babban Fasto Da Iyalansa a Jihar Delta

Yan Bindiga Sun Sace Babban Fasto Da Iyalansa a Jihar Delta

  • Miyagun ƴan bindiga sun yi awon gaba da wani babban malamin addini yana tsaka da tafiya tare da iyalansa a jihar Delta
  • Rabaran Agbadamashi Emmanuel da iyalansa sun faɗa hannun ƴan bindigan ne lokacom da suke tafiya zuwa Uwheru a ƙaramar hukumar Ughelli ta Arewa
  • Kakakin cocunan Anglican na yankin Ughelli shi ne ya tabbatar da sace babban faston amma bai bayyana ko nawa ƴan bindigan suke so ba a matsayin kuɗin fansa

Jihar Delta - Wasu ƴan bindiga sun yi garkuwa da wani Fasto na ɗarikar Anglican mai suna Rabaran Agbadamashi Emmanuel tare da matarsa ​​da ƴaƴansa a mahaɗar Evwreni da ke kan titin hanyar 'East-West' a jihar Delta.

Jaridar The Punch ta tattaro cewa lamarin ya auku ne a ranar Juma'a yayin da limamin cocin na Anglican da iyalansa su ke tafiya daga Ughelli zuwa yankin Uwheru da ke ƙaramar hukumar Ughelli ta Arewa a jihar.

Kara karanta wannan

Yan Ta'adda Sun Kai Sabon Farmaki a Jihar Arewa, Sun Yi Awon Gaba Da Manoma Masu Yawa

Yan bindiga sun sace fasto a Delta
Yan bindiga sun yi awon gaba da fasto a jihar Delta Hoto: Theguardian.com
Asali: UGC

An tattaro cewa ba zato ba tsammani kawai sai ƴan bindigan suka tare su inda suka tasa ƙeyarsu zuwa cikin daji.

Kakakin cocin Anglican na yankin Ughelli, Hon. Iyasare, shi ne ya tabbatar da aukuwar lamarin ga manema labarai a birnin Warri, babban birnin jihar Delta a ranar Litinin, 9 ga watan Oktoba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kuɗin fansa na wa ƴan bindigan suka nema?

Sai dai, bai bayar da tabbacin cewa ko ƴan bindigan sun nemi da a biya kuɗaɗen fansa ba, rahoton Daily Post ya tabbatar.

A halin da ake ciki dai malamin addinin da iyalansa na cigaba da kasancewa a tsare a hannun miyagun ƴan bindigan da suka yi awon gaba da su.

Lokacin da aka tuntubi jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sandan jihar Delta, DSP Bright Edafe, ya yi alƙawarin yin ƙarin haske da zarar ya samu bayanai daga DPO na ƴan sandan yankin.

Kara karanta wannan

Yan bindiga Sun Sake Kai Mummunan Hari a Arewacin Najeriya, Sun Halaka Mutane Masu Yawa

Mutum 2 Sun Halaka a Rikicin Manoma Da Makiyaya

A wani labarin na daban kuma, kun ji cewa an samu ɓarkewar rikici a tsakanin manoma da makiyaya a ƙauyen Kwanda na ƙaramar hukumar Ngaski ta jihar Kebbi.

Rikicin wanda ya ɓarke a tsakanin ɓanngarorin biyu ya salwantar da rayukan mutum biyu har lahira.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng