Kebbi: Mutum 2 Sun Rasa Rayukansu a Wani Rikicin Manoma Da Makiyaya
- An shiga tashin hankali a jihar Kebbi biyo bayan ɓarkewar wani rikici a tsakanin manoma da makiyaya
- Rikicin wanda ya auku a ƙauyen Kwanga na ƙaramar hukumar Ngaski ya yi sanadiyyar rasa rayukan mutum biyu
- Shugaban ƙaramar hukumar wanda ya tabbatar da aukuwar rikicin ya ce an tura jami'an tsaro domin kwantar da tarzomar da ta tashi
Jihar Kebbi - An samu ɓarkewar rikici a tsakanin manoma da makiyaya a ƙauyen Kwanga cikin ƙaramar hukumar Ngaski da ke jihar Kebbi.
Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa mutum biyu sun rasa rayukansu a rikicin da ya ɓarke tsakanin ɓangarorin biyu.
Shugaban ƙaramar hukumar Ngaski, Alhaji Abdullahi Buhari Warah, ya ce kisan da wasu mutane da ake zargin makiyaya ne suka yi wa wani manomi a gonarsa, shi ne ya sanya wasu fusatattun mutane suka kai harin ramuwar gayya a wani matsugunin Fulani inda suka kashe wani ƙaramin yaro.
Menene ya haddasa rikicin?
Ya ce faɗan ya samo asali ne sakamakon ɓarnata amfanin gona da shanu suka yi a yayin da makiyayan suka bi da su ta cikin gonakin da ke yankin, inda har ya yi sanadiyyar mutuwar mutum biyu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban ƙaramar hukumar ya ce an tura jami’an tsaro domin daƙile cigaba da kashe-kashe saboda rikicin, rahoton Analyzer News ya tabbatar.
Ya bayyana cewa babu wanda aka kama a dalilin rikicin domin manoma da makiyayan sun bar wurin kafin zuwan jami'an tsaro.
Da aka tuntuɓi jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sandan jihar, SP Nafiu Abubakar, ya ce har yanzu ba a yi masa bayani kan lamarin ba. Amma ya yi alƙawarin cewa zai kira daga baya.
Rikicin Fulani da manoma ba sabon abu ba ne a Arewacin Najeriya domin ya daɗe yana aukuwa musamman a lokutan damina.
Gwamnatin Tarayya Ta Yi Magana Kan Rikicin Falasdinu-Israila, Ta Aike Da Sako Mai Muhimmanci Ga Bangarorin 2
Yan Bindiga Sun Sace Manoma a Kaduna
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu mutane da ake kyautata zaton ƴan bindiga sun yi awon gaba da manoma 30 a ƙauyen Chikuri cikin ƙaramar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna.
Ƴan bindigan dai sun yi awon gaba da manoman ne lokacin da suka tsaka aiki da aiki a gonakinsu.
Asali: Legit.ng