Tinubu Zai Dauki Matasa Miliyan 5 Aiki a Cikin Shekaru Biyar Bayan Dakatar da Shirin N-Power

Tinubu Zai Dauki Matasa Miliyan 5 Aiki a Cikin Shekaru Biyar Bayan Dakatar da Shirin N-Power

  • Gwamnatin tarayya ta bayyana shirin da take na kawo madadin shirin N-Power da matasan kasar ke mora a baya
  • Gwamnati za ta dauki matasa sama da miliyan 5 aiki a cikin kasa da shekaru 5 masu zuwa, inji hukuma
  • Matasan Najeriya sun kadu bayan samun labarin yadda gwamnati ta dakatar da shirin N-Power da suka dogara da shi

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta kashe shirin N-Power zai samar da aikin yi ga matasa miliyan biyar nan da shekaru biyar masu zuwa a kasar nan, The Nation ta ruwaito.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Manajan shirye-shirye na N-Power, Akindele Egbuwalo ya fitar.

Egbuwalo, wanda ya bukaci ‘yan Najeriya su fahimci dalilin kashe shirin da kuma sake fasalin da ake yi, ya ce gwamnatin tarayya na kokarin kawo tsari mai kyau a shirin.

Kara karanta wannan

Mutum Miliyan 1 Sun Rasa Aikinsu Yayin da Shugaba Tinubu Ya Dakatar da N-Power

Tinubu zai dauki sabbin matasa aiki a madadin N-Power
An kashe N-Power, za a kawo sabon shiri | Hoto: Presidency
Asali: Facebook

Bayani daga mai kula da shirin N-Power

A cewarsa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Wannan gyare-gyare da sauye-sauyen zai kuma haifar da fadada shirin ya kai ga masu cin gajiyarsa masu shekaru 18-40 (a baya an kayyade shekarun zuwa 35).
"Muna da niyyar daukar mutum miliyan 5 a cikin shekaru 5 a tsarin miliyan 1 a kowace shekara a tsakanin masu digiri da wadanda ba su da digiri."

Yadda tsarin zai zama a gaba

Ya kuma bayyana yadda gwamnatin ta tsara kawo sabbin shirye-shiryen da suka hada da kimiyya, fasaha, ilimi, ayyuka noma da ma sauran bangarorin sana'a daban-daban.

Idan baku manta ba, shirin N-Power, wanda tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kawo ya ba matasa da yawa damar samun na kansu a tsawon shekaru.

Dakatar da shirin da gwamnatin Tinubu ta yi ya jawo cece-kuce da martani daga matasa da dama kafafen sada zumunta, Tribune Online ta tattaro.

Kara karanta wannan

Babu Wata Yarjejeniya Da Emefiele Kan Dawo da ‘Biliyan 50’, Gwamnatin Tinubu

Tinubu ya kashe N-Power

A tun farko kunji cewa, gwamnatin Tinubu ta yaye matasa daga nonon shirin N-Power a ranar Asabar, 7 ga watan Oktoba.

Shirin na N-Power dai ya kasance a karkashin ma'aikatar jin kai, walwala da yaki da talauci da minista Betta Edu ke jagoranta.

Ministar a tun baya ta bayyana matsayar gwamnati kan yadda za a shawo kan abubuwan da ke tattare da shirin na matasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.