Za Mu Rushe Kasuwannin Jankara, Bombata Da Pelewura, Gwamnatin Jihar Legas

Za Mu Rushe Kasuwannin Jankara, Bombata Da Pelewura, Gwamnatin Jihar Legas

  • Gwamnan jihar Legas ya bayyana cewa, zai rushe kasuwanni guda uku da ke yankin tsibirin jihar
  • Gwamnan ya kafa hujja da yadda cunkoson jama'a ya jawo gine-gine a kan magudanan ruwa a yankin
  • Jihar Legas na daga cikin jihohin da ke yawan fama da cunkoso, musamman a yankunan da ake kasuwanci

Jihar Legas - Gwamnatin jihar Legas ta bayyana aniyarta na rushe kasuwannin Jankara, Bombata da Pelewura a tsibirin Legas domin samun damar sake farfado da da fadada yankin.

Gwamna Babajide Sanwo-Olu ne bayyana hakan a jiya Asabar 7 ga watan Oktoba a lokacin da yake aikin duba ga wasu magudanan ruwa a tsibirin.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, na aikin tabbatar da aminci da tsaftar magudanan ruwa a jihar don gujewa afkuwar iftila'i.

Za a rushe kasuwanni 3 a Legas
Daya daga kasuwannin da za a rushe a Legas | Hoto: Gettu Images
Asali: Getty Images

Bayani daga gwamnan Legas kan rushe kasuwanni

Kara karanta wannan

Kotu Ta Yanke Wa Babban Malami da Ɗan Uwansa Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya Kan Abu 1

An ji gwamna Sanwo-Olu na cewa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Mun zo nan ne bisa kira kan magudanar ruwa da sake farfado da muhalli. A duk lokacin damina, gaba dayan titin Idumagbo a cika yake da ruwa saboda cunkoson da mutane ke yi, musamman daga kasuwannin yankin.
"Sun yi gini a kan magudanar ruwa saboda haka sun hana ruwa gudu, don haka muna bukatar sake ginawa gaba daya."

Za a ba 'yan kasuwa wa'adin kwashe kayayyakinsu

Sai dai, gwamnan ya ce za a ba 'yan kasuwa da wadanda ke rayuwa a yankin don su samu damar tattara kayayyakinsu, Independent ta ruwaito.

Ya kuma bayyana bukatar kasuwannin su kaura zuwa na birni da kuma bin tsarin da ba zai kawo karuwar cunkoso ba.

Jihar Legas dai jiha ce da aka fi saninta da yawan cunkoson jama'a da kuma ambaliyar ruwa a wasu yankunan.

Kara karanta wannan

Subhanallahi: Mutane Da Dama Sun Nutse a Cikin Kogi a Wani Mummunan Hatsarin Jirgin Ruwa a Jihar Arewa

Yadda Rusau a Kano ya jawo hatsaniya

A wani labarin, 'yan kasuwan da aka yiwa barnar rushewa shaguna a filin Idi na Kofar Mata a Kano, sun yi Sallah ta musamman domin neman Allah ya saka musu bisa zaluntarsu.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito yadda 'yan kasuwar suka taru don yin sallar Nafila raka'a biyu,, inda suka roki Allah ya kawo musu mafita.

Sun mika kukansu ga Allah tare da bayyana zargin gwamnatin jihar da barnata dukiyarsu ba tare da bin ka'idar da ta dace ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.