‘Sai Na Daidaita Gine-Ginensu’, Firayiministan Isra’ila Ya Sha Alwashin Kawo Karshen Hamas

‘Sai Na Daidaita Gine-Ginensu’, Firayiministan Isra’ila Ya Sha Alwashin Kawo Karshen Hamas

  • Firaministan Isra'ila ya yi alwashin karar da dakarun Hamas bayan da aka ruwaito sun kai farmaki kan Isra'ilawa
  • Ana zargin Hamas da yin sanadin mutuwar daruruwan mutane, lamarin da ya jawo cece-kuce a duniya
  • Ana ci gaba da zaman doya da manja tsakanin Isra'ila da Falasdinu, tsohuwar gabar da ke ci gaba da karuwa

Isra'ila - Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya lashi takobin kawo karshen dakarun Hamas tare da kawar da su bayan wasu hare-hare a ranar Asabar.

A cewar Netanyahu, Isra'ilawa za su ruguza Hamas tare da daukar fansa da karfi iko a yakin da ake ci gaba da gwabzawa tsakanin kasashen biyu.

Firayim Ministan ya ce dakarun Hamas suna da burin kashe dukkan 'yan Isra'ila amma gwamnatinsa ba za ta bari su yi nasara ba.

Isra'ila ta yi alwashin karar dakarun Hamas
Shugaban Isra'ila tare da dakarun sojinsa | Hoto: IsraeliPM
Asali: Twitter

Netanyahu, a cikin wani sakon da ya yada a kafar X a ranar Lahadin da ta gabata ya ce Sojojin Isra'ila za su yi amfani da karfinsu wajen tunkarar Hamas wajen mayar da inda suke boye baraguzan gine-gine.

Kara karanta wannan

Muje zuwa: Sojoji sun sheke 'yan ta'adda 31 da ke addabar al'ummar Arewa, sun kama 81

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Akalla mutum 1000 suka mutu a yakin Isra'ila da Hamas

A rahoton da muke samu, an bayyana cewa, akalla mutum 1000 ne suka rasa rayukansu a yakin da ya barke kwanan nan tsakanin Isra'ila da dakarun Hamas, rahoton NDTV.

Majiya ta bayyana cewa, farmakin da Hamas din ta kai ne musabbabin tashin yakin, wanda Isra'ila ke ci gaba da mai da martani.

Tun farko, babu jituwa tsakanin Falasdinawa da Isra'ilawa a wannan zamanin, ana yawan samun farmaki da kisan wadanda basu ji ba basu gani ba.

Isra'ila ta kashe Falasdinawa a Gaza

A bangare guda, jami'an lafiya a Gaza sun tabbatar da cewa akalla mutane 198 Falasdinawa ne suka rasa rayukansu sakamakon harin Isra'ila ta kai kan jama'ar Falasdinu.

Wannan na zuwa ne bayan Hamas ta kai farmaki kan Isra'ila da ya yi sanadin mutuwar mutane da dama a ranar Asabar.

Aljazeera ta tattaro cewa fiye da mutane 1,600 su samu raunuka yayin harin na yau Asabar 7 ga watan Oktoba a wannan shekarar da muke ciki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.