SERAP Ta Maka Akpabio Da Wasu Sanatoci 9 Kara a Gaban Kotu

SERAP Ta Maka Akpabio Da Wasu Sanatoci 9 Kara a Gaban Kotu

  • Ƙungiyar SERAP ba ta gamsu da tudu biyun da Akpabio da wasu sanatocin da tsaffin gwamnoni ne, suke ci ba
  • Ƙungiyar ta shigar da ƙara a kotu domin tilasta waɗanda ake ƙarae su daina karɓar kuɗin fansho daga jihohinsu
  • A cewar SERAP karɓar albashi tare da kuɗin fansho ya ci karo da dokar da kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanada

FCT, Abuja - Ƙungiyar SERAP ta maka shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio da wasu tsofaffin gwamnoni tara da ke a majalisar dattawa ta 10 bisa zargin karɓar kuɗaɗen fansho, yayin da suke karɓar albashi a matsayin sanatoci.

A cikin ƙarar wacce lauyoyin ƙungiyar, Kolawole Oluwadare da Ms Valentina Adegoke, suka shigar, akwai tsohon gwamna Dave Umahi, wanda tsohon Sanata ne, wanda yanzu ya zama ministan ayyuka.

Kara karanta wannan

Atiku Ya Shigar Da Sabbin Shaidun Amfani Da Takardun Bogi Kan Shugaba Tinubu, Bayanai Sun Bayyana

SERAP ta kai Akpabio da wasu sanatoci kara a kotu
SERAP na neman kotun ta hana su karbar kudin fansho Hoto: Godswill Obot Akpabio
Asali: Facebook

Sauran sanatocin da aka sanya a ƙarar su ne, Abdulaziz Yari, Aminu Tambuwal, Adamu Aliero, Adams Oshiomole, Ibrahim Gaidam, Seriake Dickson, Ibrahim Dankwambo, Aliyu Wammako da Gbenga Daniel.

Me SERAP ke nema a wajen kotun?

A cikin ƙarar mai lamba FHC/ABJ/CS/1360/2023 da ta shigar a ranar Juma'a, 6 ga watan Oktoba, a babban kotun tarayya da ke Abuja, SERAP na neman:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Kotu ta tilasta Akpabio da wasu sanatoci tara da Umahi da su daina karɓar albashi tare da kuɗin fansho. Sannan su mayar da duk wani kuɗin fansho da suka karɓa daga asusun jihohinsu."
"Kotu ta umarci Akpabio, da sauran waɗanda ake ƙara su fayyace tare da bayyana ko sun karɓa ko suna karɓa a yanzu haka albashi da kuɗin fansho a matsayinsu na tsofaffin gwamnoni."
"Kotun ta tilastawa Akpabio, da sauran waɗanda ake ƙara su bayar da cikakkun bayani bayanai da adadin kuɗaɗen fanshon da suka karba zuwa yanzu."

Kara karanta wannan

Kungiyar Hamas Ta Falasdinu Ta Kai Mummunan Hari a Isra'ila

A cikin karar, SERAP ta bayyana cewa sashe na bakwai na kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 (wanda aka gyara) ya bukaci tsofaffin gwamnoni da su daina karɓar albashi tare da fansho da kuma mayar da duk wani kuɗaɗen fansho da suka karɓa.

SERAP Ta Maka Gwamnoni Kara a Kotu

A wani labarin kuma, ƙungiyar SERAP ta maka dukkan gwamnonin Najeriya ƙara a gaban kotu.

Ƙungiyar ta maka gwamnonin ƙara ne kan tallafin cire man fetur da gwamnatin tarayya ta ba su su rabawa talakawa a jihohinsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng