Gwamna Abba Ya Kai Ziyarar Bazata a Asibiti a Kano, Ya Rabawa Majinyata N20k Kowannensu

Gwamna Abba Ya Kai Ziyarar Bazata a Asibiti a Kano, Ya Rabawa Majinyata N20k Kowannensu

  • Gwamnan jihar Kano na durowa daga birnin tarayya Abuja, ya wuce kai tsaye zuwa asibitin Sir Sanusi
  • Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kai ziyarar bazata a asibitin domin duba yanayin da asibitin yake ciki
  • Abba a yayin ziyarar ya bayar da umarnin ɗaukar wata ma'aikaciyar wucin gadi aiki na dindindin saboda yabawa da ƙoƙarinta

Jihar Kano - Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya kai ziyarar bazata a ɗaya daga manyan tsofaffin asibitocin jihar.

Gwamna Abba ya kai ziyarar bazatar ne a asibitin Sir Sanusi, wanda yake ɗaya daga cikin tsofaffin asibitocin kiwon lafiya mataki na biyu na jihar.

Gwamna Abba ya kai ziyarar bazata a asibiti
Gwamna Abba ya kai ziyarar bazata a wani asibitin Kano Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Twitter

Gwamnan wanda ya sanar da ziyarar tasa zuwa asibitin a shafinsa na X (wanda a baya aka fi sani da Twitter), ya kai ziyarar ne a daren ranar Juma'a, jim kaɗan bayan ya dawo daga birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP Ya Kai Ziyara Ta Musamman Jami'ar Tarayya Ta Gusau Kan Ɗaliban da Aka Sace

Gwamnan ya koka kan halin da asibitin yake ciki

Gwamna Abba ya bayyana cewa ya gigita kan yanayin da ya tarar da asibitin saboda yadda duk ya bi ya lalace.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Na riga na ba da umarnin gudanar da aikin gyara cikin gaggawa don tabbatar da cewa marasa lafiya da ma'aikatan lafiya suna rayuwa a ƙarƙashin yanayin da ya dace domin samar da ingantacciyar kulawa a asibitin." A cewarsa.

Ma'aikaciya ta samu aikin dindindin

A yayin ziyarar tasa gwamnan ya ci karo da wata ma'aikaciyar wucin gadi, mai suna Khadija Adam, a asibitin wacce ya yaba da yadda take ƙoƙari wajen kulawa da marasa lafiya duk da yanayin rashin kyau da asibitin yake ciki.

Yabawa da ƙoƙarin da Khadija take yi a asibitin ya sanya gwamnan ya bayar da umarni a ɗauketa aiki a matsayin ma'aikaciya ta dindindin a nan take.

Kara karanta wannan

Babbar Matsala 1 Da Aka Gano Bayan Taron da Atiku Ya Gudanar Kan Shugaba Tinubu a Abuja

Haka kuma gwamnan ya rabawa dukkan majinyatan da ke kwance a asibitin kuɗi naira dubu ashirin, a matsayin agajin gaggawa.

Dan Majalisar NNPP Ya Yi Nasara a Kotu

A wani labarin kuma, kotun ɗaukaka ƙara ta dawo da kujerar ɗan majalisar da ke wakiltar Tarauni na jam!iyyar NNPP da kotun zaɓe ta ƙwace a watan Agusta.

Mukhtar Umar Yarima ya samu nasara a kotun ɗaukaka ƙarar bayan rashin gamsuwa da hukuncin kotun zaɓen ta yanke.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng