“Ta Shirya”: Wasu Yan Mata 3 Sun Saka Yayarsu a Kasuwa, Sun Bukaci Maza Su Nemi Aurenta
- Wasu yan Najeriya sun saka yayarsu da bata da mashinshini a kasuwa a kokarinsu na taimaka mata wajen samun abokin rayuwa
- A cewar daya daga cikin yan matan, yayarsu bata da tabbacin samun saurayi domin dai bata fita daga gida
- Yan matan sun bukaci samari da ke ganiyar shekaru 30 da doriya da su nemi aurenta, suna masu cewa ta shirya yin aure
Domin taimakawa yayarsu wajen samu mijin aure, wasu yan mata uku sun tallata ta a soshiyal midiya.
Daya daga cikin yan matan mai suna, @Nashbals, ta wallafa hotunan yayar tasu a dandalin X, tana mai cewa sun yanke shawarar cewa lokaci ya yi da ya kamata su sakata a kasuwa.
@Nashbals ta rubuta cewa yayarsu na neman miji kuma bata da tabbaccin samu domin dai a kullun tana kunshe ne a cikin gida.
Ta karfafawa samari da ke ganiyar shekaru talati da doriya da su nemi aurenta a shafinta mai suna @Antieprecious. Ta rubuta:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Barka dai jama'a, Ni da yan uwana mata biyu mun yanke shawarar sanya yayarmu a kasuwa!
"Bata da saurayi, tana nema, bata taba barin gida kuma ta shirya yin tarayya harma ta shiga daga ciki nan da watanni 6.
"Don Allah maza da ke shekaru 30 da doriya su nemi aurenta. A tura sako."
Kalli wallafarta a kasa:
Jama'a sun yi martani
@A_RWAC ya ce:
"Don soyayya da ni, tana bukatar kawo bunsuru masu farin gemu guda 17 da katafaren gida a Lekki, ban tambayi abu da yawa ba."
@geesnaturals ta ce:
"Kai kanne mata mutum ba zai yi rashin saurayi hankali kwance ba, ina tausaya mata, ina fatan maza masu kyakkyawar niya za su zo gareta."
@TocsWears ta ce:
"Shakka babu za ta yi aure kafin Disamba, ku rubuta ku ajiye amma dole sai ta yi abun da ya kamata, kina iya aika mani sako don na nuna maki hanya."
Matar aure ta yi wa mijinta wanka da ruwa yana tsaka da bacci
A wani labari na daban, wani bidiyo na wata matar aure da ke kwararawa mijinta da ke bacci ruwa ya haifar da zazzafan martani a soshiyal midiya.
Bidiyon wanda @SanphuSA ya wallafa a dandalin X ya yi fice, inda mutane da dama suka yi Allah wadai da abun da matar ta yi.
Asali: Legit.ng