An Bayyana Dalilin Da Ya Sanya Yan Bindiga Suka Sace Daliban FUDMA

An Bayyana Dalilin Da Ya Sanya Yan Bindiga Suka Sace Daliban FUDMA

  • Mataimakin shugaban jami'ar gwamnatin tarayya da ke Dutsinma (FUDMA) a jihar Katsina, ya bayyana dalilin sace ɗalibai a jami'ar
  • Armaya'u Bichi ya bayyana cewa ƴan bindigan da suka sace su ramuwar gayya suka zo yi kan harin da jami'an tsaro suka kai musu
  • Bichi ya ƙara da cewa jami'an tsaro na bakin ƙoƙarinsu domin ganin cewa ɗaliban sun shaƙi iskar ƴanci

Jihar Katsina - Yan ta’addan da suka sace ɗalibai biyar na jami'ar tarayya da ke Dutsinma a jihar Katsina, ramuwar gayya suka je yi.

Mataimakin shugaban jami'ar, Armaya'u Bichi ya bayyana cewa ƴan bindigan sun sace ɗaliban ne domin ramuwar gayya kan harin da jami'an tsaro suka kai kan wasu ƴan uwan mambobinsu.

An bayyana dalilin sace daliban FUDMA
An bayyana dalilin yan bindiga na sace daliban FUDMA Hoto: FUDMA
Asali: Twitter

Premium Times ta rahoto cewa Farfesa Bichi, yayin wata tattaunawa da DW Hausa a yammacin ranar Juma'a, 6 ga watan Oktoba, ya ce masu garkuwar sun bayyana dalilin yin garkuwa da daliban a wata tattaunawa domin ganin an sako su.

Kara karanta wannan

Majalisar Dattawa Ta Ɗauki Mataki Mai Jan Hankali Kan Sace Ɗalibai Mata a Jami'ar Arewacin Najeriya

An sace ɗaliban ne a ranar Larabar da ta gabata a lokacin da ƴan ta'addan suka kai farmaki gidansu da ke unguwar Mariamoh Ajiri a cikin garin Dutsin Ma.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ko ƴan bindigan sun buƙaci kuɗin fansa?

Farfesa Bichi, bai bayyana ko ƴan ta'addan sun buƙaci a biya su kuɗin fansa domin a sako ɗaliban ba.

A kalamansa:

"Ana ci gaba da tattaunawa da su (ƴan ta'adda). Hukumomin tsaro suna yin iya bakin ƙoƙarinsu (don kuɓutar da ɗaliban). Su (ƴan ta'addan) sun yi magana kuma sun ce ramuwar gayya ce ta kai wa iyayensu hari a ƙaramar hukumar Batsari. An ƙona gidaje na iyayensu tare da kwashe shanunsu da kuma hatsi."
"Sun so su rama harin da aka kai a Batsari amma wani shugaban ƙungiyar ƴan ta’adda bai goyi bayansu ba inda ya hana su, shi ne sai suka zo Dutsin Ma domin ɗaukar fansa."

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Yan Bindiga Sun Sake Sace Dalibai Mata a Wata Babbar Jami'a a Arewacin Najeriya

"Amma su (ƴan ta'adda) an gaya musu gaskiya cewa mutanen Dutsinma da daliban ba su yi musu laifi ba don haka su sako daliban da aka sace. Mun yi imanin cewa da yardar Allah za su sake su."

An Cafke Dan Leken Asirin Yan Bindiga

A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar ƴan sanda jihar Katsina ta tabbatar da cafke wani da ake zargi da hannunsa a wajen sace ɗaliban jamiar FUDMA.

Rundunar ta bayyana cewa ta kama wani da ke da hannu wanda kuma ake zargin shi ne mai bai wa ƴan bindigan bayanan sirri da su ka sace ɗaliban.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel