Hukumar INEC Ta Janye Daukaka Karar Da Ta Yi Kan Hukuncin Zaben Gwamnan Kano

Hukumar INEC Ta Janye Daukaka Karar Da Ta Yi Kan Hukuncin Zaben Gwamnan Kano

  • Hukumar zaɓe ta ƙasa ba za ta cigaba da neman daukaka ƙara ba kan hukuncin da kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan Kano ta yanke
  • Hakan na ƙunshe ne a cikin wata takarda mai ɗauke da sa hannun shugaban sashin shari’a na hukumar a ranar Juma’a 6 ga watan Oktoba
  • A cikin takardar dai an tabbatar da cewa umarnin janye ƙarar ya fito ne daga hedikwatar hukumar da ke Abuja

Jihar Kano - Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta janye ƙarar da ta ɗaukaka kan hukuncin da kotun sauraron ƙararrakin zaben gwamnan Kano ta yanke.

An tabbatar da hakan ne a wata wasiƙa mai dauke da sa hannun Suleiman Alkali, shugaban sashin shari’a na hukumar a Kano, a ranar Juma’a, 6 ga watan Oktoba.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Ɗumi: Kotun Zaɓe Ta Yanke Hukunci Kan Nasarar Gwamnan LP a Zaben 2023

INEC ta janye karar da ta daukaka kan hukuncin zaben gwamnan Kano
Hukumar INEC ta fasa daukaka kara kan hukuncin zaben gwamnan Kano Hoto: Olukayode Jaiyeola
Asali: Getty Images

Kamar yadda Daily Nigerian ta rahoto, wasiƙar na cewa:

"Hedikwatar hukumar INEC ta umurce ni da cewa a hukumance ba ta da wani dalili na ɗaukaka ƙara kan wannan hukunci."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Saboda haka, sashen hukumar da ke kula da harkokin shari'a da kuma kwamishinan hukumar na ƙasa mai kula da shiyyar Kano sun ba da umarnin a janye ƙarar, kuma a mika duk wani tsari na duk ɗaukaka ƙara ga ofishin Kano."

INEC ta ɗaukaka ƙara

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta shigar da ƙara kan hukuncin kotun, inda ta ce kotun sauraron ƙararrakin zabe ta yi kuskure a cikin doka inda ta ayyana ɗan takarar masu shigar da ƙara, wanda ba ya cikin ƙarar a matsayin wanda ya lashe zaɓen.

Idan za’a tuna a ranar Litinin 29 ga watan Mayu ne aka rantsar da gwamna Yusuf bayan da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa INEC ta bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna a jihar Kano, kuma hukumar zaɓe ta miƙa masa takardar shaidar cin zabe.

Kara karanta wannan

Kano: DSS Ta Kama Matar da Ta Yi Barazanar Kashe Mataimakin Tinubu, Gawuna da Alƙalai a Bidiyo

Abba Ya Dauko Hayar Lauyan Tinubu

A wani labarin kuma, gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ɗauko hayar lauyan da ya kare Tinubu a shari'ar zaɓen shugaban ƙasa.

Wole Olanipekun zai kare gwamnan a ƙarar da ya ɗaukaka bayan kotun zaɓen gwamnan Kano ta ƙwace nasararsa a matsayin gwamnan Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng