“Babu Kwana-Kwana”: Matashi Ya Yi Wa Budurwa Alkawarin Miliyan 1 a Dare Daya, Ta Yi Martani
- Budurwa yar Najeriya ta saki hoton sako mai rikitarwa da ta samu daga wani mutum mai suna Lars Eugene
- Lars ya yi alkawarin ba kyakkyawar budurwar kudi masu yawa idan ta yarda ta kwana da shi
- Lamarin mai ban tsoro ya haifar da zazzafan muhawara kan cin zarafi da kuma mahimmancin neman kariya ga mata
Wata matashiyar budurwa yar Najeriya, Okoli Classic, ta samu sakon imel a kwanan nan daga wani mutum mai suna Lars Eugene.
A cikin sakon nasa, mutumin ya yi magana kai tsaye ba tare da kwana-kwana ba sannan ya bayyana kansa a matsayin mai bibiyar shafin Tunde Ednut.
Matashi ya fito fili ya ce zai ba budurwa miliyan 1 a dare daya
Da yake ci gaba da magana, mutumin ya ce zai ba budurwar kudi naira miliyan 1 idan har ta yarda suka kwana tare.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sakon ya ce:
"Barka dai kyakkyawa, Na gano ki ne a shafin Tunde Ednut. Kawai ina so na tambaya ne, shin za ki iya kwana da ni kan naira miliyan 1?"
Bayan dan lokaci, ya sake aika mata da wani imel din, yana mai kara kudin da kuma tsara otel din da za su iya karba a Lagas.
Ya kara da cewar:
"Barka dai. Kawai ina so na sani ko kin amince ko kin canja shawara? Ina iya kara kudin idan ba za ki damu ba. Kuma ina iya fara tura maki wani bangare na kudin don ki san da gaske nake. Daga nan sai mu karbi hadadden dakin otel a Lagas. Ina jiran amsarki."
Da take martani ga wannan, Okoli ta saki hoton hirar tana mai kokawa kan cewa tana samun irin wadannan sakonnin tun bayan da ta zama fitacciya.
Okoli Classic ta yi suna ne bayan mawaki Davido ya yi mata kyautar naira miliyan 2 saboda ta sa shi nishadi da bidiyonta.
Jama'a sun yi martani
@commanderr_tom ya yi martani:
"Toh me ya shafe mu da wannan wallafar? Idan kin amince za ki raba kudinki da mu ne. Ko yaya dai. Ki yi mun karin bayani kan labarin. Ina son tsegumi."
@chocol8quin ta yi martani:
"Da wannan hali da ake ciki a Najeriya a yanzu zan je hankali kwance. Amma kafin na je dole yan uwa da abokaina su kasance da hotonsa koda na dawo babu wani sassa na jikina ko kuma ban dawo ba."
@iamblackbharbie22 ta yi martani:
"Mutumin nan ba shi ma da wannan kudin. Kawai yana so ya ja hankalin yarinyar ne."
@florenceslim ta ce:
"Don Allah ki karbi kudin tukuna."
Kalli bidiyon a kasa:
Matashi zai yi wuff da kyawawan yan mata 2 a ranar daya
Namijin Duniya: Wani Dattijo Ya Tsara Budurwa a Waya, Ya Yi Alkawarin Mallaka Mata Zuciyarsa Kacokan
A wani labarin, mun ji cewa wani matashi dan Najeriya mai suna Prince Okebulu Ndukwo Nkobi, daga Abiriba a karamar hukumar Ohafia ta jihar Abia, ya shirya tsaf domin auren wasu kyawawan yan mata biyu a rana daya.
Za a daura auren ne a ranar 19 ga watan Nuwamban 2023, a harabar gidan iyalin Nkobi da ke garin Abariba.
Asali: Legit.ng