Gobara Ta Salwantar Da Rayukan Mutum 6 a Jihar Kano
- Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta sanar da adadin yawan mutanen da suka rasa ransu a jihar a cikin watan Satumban 2023
- Jami'in hulɗa da jama'a na hukumar ya bayyana cewa mutum shida ne suka rasa rayukansu a jihar a dalilin gobara daban-daban da ta tashi
- Saminu Abdullahi ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa inda ya ce sama da dukiyar da ta kai ta naira miliyan 23 aka yi asara a dalilin gobara a jihar
Jihar Kano - Hukumar kashe gobara ta jihar Kano a ranar Juma’a, 6 ga watan Oktoba, ta bayyana cewa mutum shida sun ƙone kurmus tare da lalata kadarori na naira miliyan 23 a gobara daban-daban da aka yi a jihar a watan Satumba, 2023.
Hukumar kashe gobara ta kuma bayyana cewa an ceto kadarorin da darajarsu ta kai naira miliyan 34 a cikin gobara 21 da aka samu a jihar.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da jami'in hulɗa da jama'a na hukumar, Saminu Abdullahi, ya fitar a Kano, cewar rahoton PM News.
Rayukan mutum nawa hukumar ta ceto?
Abdullahi ya bayyana cewa an kuma ceci rayuka 17 a cikin lokacin na watan Satumba da ake magana a kai.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Hukumar ta amsa kiraye-kirayen ceto guda 16 da kuma kirayen-kirayen ƙarya guda shida daga mazauna jihar." A cewarsa.
Kakakin hukumar ya shawarci masu ababen hawa da su guji amfani da silinda man iskar gas na LPG a cikin motocinsu da janareta domin gujewa tashin gobara.
"Maimakon hakan a nemi tulun iskar gas na CNG" A cewar Abdullahi.
Ya kuma shawarci jama’a da su riƙa kula da wuta tare da cigaba da share magudanun ruwa domin gujewa abubuwan da ba a zata ba.
Subhanallahi: Mutane Da Dama Sun Nutse a Cikin Kogi a Wani Mummunan Hatsarin Jirgin Ruwa a Jihar Arewa
Gobara Ta Tashi a Kamfanin Robobi
A wani labarin kuma da ya zo muku a baya, kun ji cewa wata mummunar gobara ta tashi a wani babban kamfanin sarrafa robobi da ke a jihar Legas.
Mummunar gobarar dai ta tashi ne a kamfanin sarrafa robobi na Mega Plastics da ke a kusa da kwanar titin Ilupeju a yankin Mushin na jihar Legas.
Asali: Legit.ng