Dantata Da Wasu Attajirai 3 Sun Samu Kwangiloli Masu Gwabi Daga NNPC
- Kamfanin mai na ƙasa NNPC ya bayar da kwangilar gyaran bututun mai ga wasu kamfanonin mai na cikin gida guda huɗu
- Waɗannan kwangiloli suna da matukar muhimmanci ga tsarin samar da makamashi a Najeriya yayin da Najeriya ta rage dogaro da shigo da kayayyaki daga ƙasashen waje
- Masu ruwa da tsaki na ganin cewa aikin bututun mai ya sha bamban da kasuwancin siyar da mai
Wasu hamshaƙan attajirai guda huɗu na Najeriya na shirin samun kuɗaɗe masu kauri bayan kamfanoninsu sun samu kwangiloli na biliyoyin kuɗi daga kamfanin man fetur na ƙasa (NNPC).
Kamfanonin sun haɗa da Oilserv Limited, A.A RANO Nigeria Limited, Macready Oil & Gas Service Company Limited, da MRS Oil Nigeria.
Waɗannan kwangilolin, waɗanda aka bayar ta hanyar tsarin kuɗi na ginawa, aiki, da mayarwa hannun gwamnati, an tsara su don sauƙaƙe wadatar ɗanyen mai ga matatun mai da fitar da tataccen mai daga gare su.
Kamfanonin kuma za su kula da kuma gyara faffaɗan bututun mai a faɗin ƙasar nan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Cikakken bayani kan kwangilolin bututun mai na NNPC
Jaridar Businessday ta bayar da rahoton cewa, layin bututun ya ƙunshi bututun mai wanda ke da tsawon kilomita 4.35 da kuma bututun ɗanyen mai wanda ke da tsawon kilomita 701.
Haka kuma ta haɗa ma'ajiyar mai guda 22, da matatun mai guda huɗu na Najeriya, da kuma bututun mai masu muhimmanci na Atlas Cove da Warri.
Yadda kwangilolin suke
Ga yadda tsarin kwangilolin da aka baiwa kamfanonin huɗu yake:
Oilserv Limited
Oilserv Limited, mallakar Injiniya Dr. Emeka Okwuosa ya samu kwangilar LOT 1 da suka haɗa da bututun danyen mai na Bonny-Port Harcourt, bututun kayayyaki na Fatakwal-Aba-Enugu, da dai sauransu.
A.A. RANO
Kamfanin Alhaji Auwalu Abdullahi Rano ya samu LOT 2, wanda ya haɗa da bututun ɗanyen mai na Escravos-Warri, bututun kayayyaki na Warri-Benin, da sauran su.
Macready
Kamfanin Macready Oil & Gas, wanda mallakin Olu Fagbemi ne, zai kula da LOT 3, wanda ya shafi bututun ɗanyen mai na Warri-Kaduna, bututun kayayyaki na Kaduna-Kano, da dai sauransu.
MRS Oil Nigeria Plc
MRS Oil Nigeria, wanda Alhaji Sayyu Dantata ya kafa a shekarar 1995, ya samu LOT 4, wanda ya haɗa da bututun mai na Atlas Cove-Mosimi/Satellite, bututun kayayyaki na Mosimi-Ore, da sauran su.
Damuwa daga masu ruwa da tsaki a masana'antar
Masu ruwa da tsaki a masana'antar sun nuna damuwa game da zabin MRS da Rano da NNPC ya yi, suna masu cewa dillalan ba su da dangantaka da kwangilar bututun mai.
Babu Shirin Kara Farashin Mai, NNPC
A wani labarin kuma, kamfanin man fetur na ƙasa (NNPC) ya musanta batun cewa yana shirin ƙara farashin man fetur.
Kamfanin NNPC wanda ke ƙarƙashin gwamnatin tarayya ya ce ba shi da niyyar ƙara farashin fetur kamar yadda ake ta yaɗa wa a soshiyal midiya.
Asali: Legit.ng