Wajen Fallasa Tinubu, Atiku Ya Fadi Yadda Buhari Ya Durkusar da Kasuwancinsa
- Atiku Abubakar ya nuna bai tsoron ya rasa komai a gwamnati a dalilin fadansa da Bola Ahmed Tinubu
- ‘Dan takaran PDP a zaben shugaban kasa ya hakikance a kan sai kotun koli ta tsige shugaban Najeriya
- Wazirin Adamawa ya bayyana cewa Muhammadu Buhari ya na hawa mulki, ya taso kamfaninsa a gaba
Abuja - A ranar Alhamis, 5 ga watan Oktoba 2023, Atiku Abubakar ya tara manema labarai, ya yi jawabi a kan badakalar Bola Tinubu.
Atiku Abubakar wanda ya zo na bayan Bola Tinubu a zaben shugaban kasa, ya zargi shugaban Najeriyan da amfani da takardun bogi.
Yayin da yake jawabi a birnin Abuja, Wazirin Adamawa ya yi bayanin yadda gwamnatin baya ta rusa kasuwancin da yake yi.
Muhammadu Buhari ya karya Atiku Abubakar
'Dan kasuwan ya ce Muhammadu Buhari ya na zama shugaban kasa, ya yi sanadiyyar soke kwangilar da aka yi da kamfaninsa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
‘Dan takaran jam’iyyar PDP ya shaida cewa duk da bai aiki da kamfanonin mai, ya na wasu kasuwancin da su ka shafi noma da sauransu.
Tsohon mataimakin shugaban na Najeriya ya bayyana cewa ko da shugaban kasa Buhari ya soke kwangilarsa, ya rabawa mutanensa ne.
A jawabin da ya gabatar wanda Premium Times ta wallafa, Atiku bai fadi wadanda su ka amfana da kwangilar a tsohuwar gwamnatin ba.
Atiku bai tsoron gwamnatin Tinubu
"Gwamnatin Muhammadu Buhari ta na zuwa, duk da mu na da lasisi, babu abin da ya hada mu da gwamnati, ‘yan kwangila ne mu kurum masu yi wa kamfanonin mai jigila, ba gwamnati ba.
Amma gwamnatin Muhammadu Buhari ta na zuwa, sai aka karbe duka wadannan kamfanoni daga hannunmu, saboda haka ba na wata hulda da gwamnati.
A dalilin haka ba na tsoron a karbe wani kasuwanci daga hannu na, an riga an karbe tun da Buhari ya karbi mulki, sun raba a junansu.
- Atiku Abubakar
Batun takardun Bola Tinubu
Doka ta hana wanda aka samu da takardar shaidar bogi tsayawa takarar shugaban kasa, ku na da labari ana zargin Bola Tinubu da wannan.
Atiku Abubakar ya na ikirarin Shugaban kasa ya gabatarwa INEC da takardun karatun bogi, saboda haka yake so kotun koli ta tsige shi.
Asali: Legit.ng