Manyan kamfanoni 4 da Atiku Abubakar ya mallaka a ciki da wajen Najeriya

Manyan kamfanoni 4 da Atiku Abubakar ya mallaka a ciki da wajen Najeriya

Atiku Abubakar dai dan asalin wani gari ne da ake kira Jada, jihar Adamawa kuma an haife shi ne a ranar 25 ga watan Nuwamba, 1946 kuma shi kadai ne ya rayu a cikin 'ya'yan da mahaifan sa suka haifa a tare.

Labarin da muke samu da dumin sa yanzu na nuni ne da cewa tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya Alhaji Atiku Abubakar ne ya lashe zaben fitar da gwanin jam'iyyar PDP ta gabatar.

Manyan kamfanoni 4 da Atiku Abubakar ya mallaka a ciki da wajen Najeriya
Manyan kamfanoni 4 da Atiku Abubakar ya mallaka a ciki da wajen Najeriya
Asali: Depositphotos

Legit.ng ta samu cewa yanzu dai biyo bayan lashe wannan zaben, Atiku Abubakar ne zai kara da shugaba Buhari na APC a zaben 2019 mai zuwa.

A shekarar 2014 dai, Atiku Abubakar din ya taba lissafa yawan kamfanonin sa manya a ciki da wajen kasar nan kuma gasu kamar haka:

1. Kamfanin Intels

Kamfanin Intels dai yana harkokin da suka shafi dakon kaya ne a bangaren mai, da kuma tashoshin jiragen ruwa na Najeriya.

2. Prodeco

Kamfanin Prodeco shi kuma babban kamfani ne da yake harkokin gine-gine da kuma hakar ma'adanai kamar su danyen mai da dai sauran su.

3. Gonar Atiku Abubakar

Haka zalika Atiku yace yana da makekiyar gona a jihar Adamawa da takai murabba'in eka 2,500 wadda kuma ake harkokin noma da kiwo a cikin ta.

4. Makarantun ABTI

Wannan kuma makarantu ne da kamfanin ya bude hadin gwuiwa da jami'oin kasar Amurka da kuma suke a wurare da dama cikin Najeriya ciki kuwa hadda jami'a a garin Yola, jihar Adamawa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng