Gwamna Lawal Ya Ziyarci Jami'ar Tarayya Ta Gusau Kan Daliban da Aka Sace

Gwamna Lawal Ya Ziyarci Jami'ar Tarayya Ta Gusau Kan Daliban da Aka Sace

  • Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya kai ziyara jami'ar tarayya ta Gusau kan batun sace ɗalibai mata sama da 20
  • Lawal na jam'iyyar PDP ya tabbatar wa mahukuntar jami'ar cewa hukumomin tsaro na iya bakin kokarinsu wajen ceto ɗaliban
  • Wani ɗalibin jami'ar ya shaida wa Legit Hausa cewa gwamnan ya kai musu ziyara ta biyu kenan a jere bayan abinda ya faru

Jihar Zamfara - Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ba da tabbacin cewa jami’an tsaro na bakin kokarinsu wajen ganin an ceto daliban jami’ar tarayya ta Gusau da aka sace.

Ya kuma yi alkawarin samar da isasshen tsaro a jami’ar domin daliban su ci gaba da gudanar da harkokinsu na neman ilimi ba tare da fargabar harin 'yan ta'adda ba.

Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara.
Gwamna Lawal Ya Ziyarci Jami'ar Tarayya Ta Gusau Kan Daliban da Aka Sace Hoto: Dauda Lawal
Asali: Facebook

Gwamnan ya bayar da wannan tabbacin ne a ranar Alhamis yayin da ya kai ziyara domin gane wa idonsa yanayin al’amuran tsaro a jami’ar da kewaye, Channels tv ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Majalisar Dattawa Ta Ɗauki Mataki Mai Jan Hankali Kan Sace Ɗalibai Mata a Jami'ar Arewacin Najeriya

Dauda Lawal ya kai wannan ziyara ne biyo bayan sace ɗalibai mata sama da 20 a gidan kwanansu da ke ƙauyen Sabon Gida, jihar Zamfara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan bindiga sun aikta wannan ɗanyen aike ne a lokacin da gwamnan ba ya cikin Zamfara, amma daga dawowarsa ya dira makarantar domin gane wa idonsa halin da ake ciki.

Ya kuma karɓi bayanai daga shugabannin makarantar ta yadda zasu haɗa karfi da ƙarfe wajen inganta tsarin tsaro a jami'ar, Vanguard ta ruwaito.

Ya dauki lokaci ya na jawabi ga daliban jami'ar, inda ya bukace su da kada su bari wannan yanayi mara dadi ya kashe musu guiwa wajen ci gaba da karatunsu.

Gaskiya gwamna yana ƙoƙari - Ɗalibi

Wani ɗalibin aji biyu a jami'ar tarayya da ke Gusau ya shaida wa Legit Hausa ta wayar salula cewa Gwamnan Zamfara na kokari sosai bayan abinda ya faru.

Kara karanta wannan

Gwamnan Benue Ya Bayyana Adadin Kudin Fansan Da Aka Biya Kafin Sakin Kwamishinansa Da Aka Sace

Ɗalibin ɗan asalin jihar Katsina, wanda ya nemi a sakaya bayanansa saboda tsaro ya ce:

"A zahirin gaskiya gwamna Lawal yana kokari, ya zo jiya kuma yau ma ya dawo, ya faɗa mana yana kokarin ganin an girke dakarun soji a makaranta domin a bamu tsaro."
"Ya nuna damuwarsa sosai kuma mun ji daɗi. Dangane da waɗanda ke hannun 'yan ta'adda kuma gaskiya ba mu ji labarin komai ba."

Gwamnoni da Jiga-Jigan PDP Ba Su Halarci Taron da Atiku Ya Gudanar Ba

A wani rahoton kuma Taron manema labaran da Atiku ya gudanar ya ƙara nuna cewa har yanzun wutar rikici na ci gaba da ruruwa a jam'iyyar PDP.

Abun mamakin shi ne babu ko gwamna ɗaya daga cikin gwamnonin PDP 13 masu ci ko yan majalisar da suka halarci wurin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262