Daga Karshe, An Gano Shugaban Fulani da Ya Bata a A Jihar Filato a Mace
- Dakarun soji sun gano gawar shugaban Fulanin da ya ɓata tun watan Satumba a jihar Filato da ke Arewa ta Tsakiya
- Shugaban MACBAN reshen jihar da rundunar Operation Save Haven sun tabbatar da gano gawar Ardo Adamu Idris
- A ranar 24 ga watan Satumba, 2023 aka ayyana ɓatan Arɗo kuma COAS ya umarci Sojoji su nemo shi duk inda ya ke
Plateau - An gano gawar Arɗo, shugaban Fulani na gundumar Panyam a karamar hukumar Mangu da ke jihar Filato, Adamu Idris, wanda ya ɓata a kwanakin baya.
Shugaban kungiyar Fulani Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria (MACBAN) reshen jihar Filato, Nuru Abdullahi, shi ne ya tabbatar da gano gawar.
Ya bayyana cewa za a masa jana'iza kamar yadda addini ya tanada a jihar Bauchi da ke Arewa maso Gabashin Najeriya, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Kano: Duk da Kotu Ta Tsige Shi, Abba Gida-Gida Ya Bada Hutun Kwana Ɗaya Na Murnar Haihuwar Annabi SAW
Shugaban kungiyar ta MACBAN ya ce an gano gawar Arɗon ne a ƙauyen Dawaki da ke yankin ƙaramar hukumar Kanke a jihar Filato.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kakakin rundunar ‘Operation Safe Haven’ da ke wanzar da zaman lafiya a yakin jihar Filato, Captain Oya James, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Yadda Ardo Idris ya ɓace a watan Satumba
Idan baku manta ba, babban hafsan rundunar sojin ƙasa ta Najeriya, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja, ya bada umarnin gaggauta nemo gawar shugaban Fulanin a ko ina take.
A ranar 27 ga watan Satumba, 2023, Shugaban hukumar sojin ya bai wa dakarun sojin rundunar Operation Save Haven umarnin zaƙulo gawar mutumin cikin awanni 24 kaɗai.
Kwana biyu gabanin haka watau ranar 25 ga watan Satumba, aka bayyana cewa Arɗo Adamu Idris, ya ɓata ba a san inda ya shiga ba domin bai koma gida ba.
An tattaro cewa shugaban Fulanin ya bata ne a daidai lokacin da yake kan hanyar koma wa gida bayan ya ziyarci hakimin yankin, Aminu Darwam, Daily Post ta ruwaito.
Mohbad: Primeboy Ya Mika Kansa Ga Yan Sanda Bayan Ayyana Nemansa Ruwa a Jallo
A wani rahoton kuma Primeboy, abokin fitaccen mawaƙin nan da ya mutu Mohbad ya miƙa kansa ga rundunar yan sandan jihar Legas.
Wannan na zuwa ne bayan rundunar 'yan sanda ta ayyana nemansa ruwa a jallo kuma ta sanya ladan Naira miliyan ɗaya ga duk wanda ya taimaka.
Asali: Legit.ng