Tinubu Ya Yi Alkawarin Inganta Rayuwar Malamai A Najeriya
- Yayin da ake bikin ranar malamai ta duniya, Shugaba Tinubu ya yi alkawari ga malaman Najeriya
- Tinubu ya yi alkawarin saka wa malamai tun a duniya ganin irin tasirin da su ke da shi wurin inganta rayuwar al'umma
- Shugaban ya ce babu wata hanya da ke saurin sauya akalar rayuwar al'umma ta hanya mai kyau kamar ilimi
FCT, Abuja - Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi alkawarin saka wa malamai a irin kokarin da su ke yi na inganta harkokin ilimi.
Tinubu ya bayyana haka ne a yau Alhamis 5 ga watan Oktoba a shafinsa na Twitter.
Wane alkawari Tinubu ya yi ga malamai?
Shugaban ya fadi haka ne yayin ya ke taya al'ummar Najeriya bikin ranar malamai ta duniya a yau Alhamis, Tribune ta tattaro.
Alkalai Sun Shiga Taitayinsu Yayin Da CJN Ariwoola Ya Tura Musu Muhimmin Sako Na Jan Hankali Kan Yanke Hukunci
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce babu wata hanyar tsira da ke da tasiri a rayuwar al'umma kamar ilimi a kasa.
Ya kara da cewa a karkashin mulkinsa zai bai wa malamai da harkar ilimi kulawa na musamman don inganta rayuwar al'ummar kasar.
Ya ce:
"Na yi imanin cewa babu wata mota da za ta kai ka inda ka ke so lafiya kamar harkar ilimi.
"Wannan na daga cikin dalilan da su ka sa ko wane yaro a kasar duk yadda matakinsa ya ke a rayuwa ke saka tsammanin samun damarmaki a nan gaba."
Meye Tinubu ya ce kan inganta ilimi da malamai?
Tinubu ya ce ilimi ne kadai ke sauya akalar rayuwar mutane a kankanin lokaci ba tare da tsaiko ba, cewar Vanguard.
Ya kara da cewa:
"Yayin da mu ke bikin ranar malamai ta duniya, ina mai tabbatar muku cewa gwamnatina za ta yi duk mai yiyuwa don saka wa malamai.
"Ilimi ne kadai ke sauya rayuwar al'umma ko iyalai cikin kankanin lokaci da al'ajabi."
A kokarin inganta rayuwar ma'aikata, Tinubu ya kara Naira dubu 35 a albashin ma'aikata don rage musu radadin cire tallafi.
Wannan na zuwa ne bayan Kungiyar Kwadago ta NLC ta yi barazanar shiga yajin aiki a wannan mako.
NLC ta yi wa ma'aikata albishir
A wani labarin, Kungiyar NLC ta yi wa ma'aikata albishir na sabon mafi karancin albashi.
Kungiyar ta ce a tattaunawar da za ta yi nan gaba za ta bukaci dubu 100 zuwa 200 mafi karancin albashi.
Asali: Legit.ng