Kotun Ta Yanke Wa Fasto da Dan Uwansa Hukuncin Kisa Ta Hanyar Ritaya

Kotun Ta Yanke Wa Fasto da Dan Uwansa Hukuncin Kisa Ta Hanyar Ritaya

  • Babbar Kotu a jihar Akwa Ibom ta yanke wa Malamin addini da ɗan uwansa hukuncin kisa ta hanyar rataya
  • An yanke musu wannan hukuncin ne bayan kama su da aikata laifin kisan wani manomi da gangan kan rigimar gona
  • Alkalin Kotu ya ce masu shigar da ƙara sun gamsar da Kotu cewa tabbas waɗan da ake zargi sun aikata wannan ɗanyen aiki

Akwa Ibom - Babbar kotun jihar Akwa Ibom da ke zama a Essien Udim ta yanke wa wasu ’yan uwan juna, Fasto da direban babur, hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa laifin kashe wani manomi a kan fili.

Wadanda aka yankewa hukuncin su ne Uduak Udo Umoren, malamin coci ɗan shekara 48 da ɗan uwansa, Emmanuel Udo Umoren, mai shekaru 34, wanda aka fi sani da ‘okada’.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Kai Sabon Hari a Jihar Arewa, Sun Halaka Babban Kusan Gwamnati

Kotu ta yanke wa Fasto hukuncin kisa.
Kotun Ta Yanke Wa Fasto da Dan Uwansa Hukuncin Kisa Ta Hanyar Ritaya Hoto: dailytrust
Asali: UGC

An same su da laifin kashe wani, Iboro Akpan Joe, mai shekaru 45 manomi kuma ɗan kasuwa daga garin Ikot Otu dake karamar hukumar Essien Udim a jihar, Daily Trust ta ruwaito.

Yadda lamarin ya faru tun farko

An tattaro cewa Joe ya raka surukarsa zuwa gonar marigayin mijinta domin tantance ko nawa za ta sayar da filin tare da yin amfani da kudaden da aka samu wajen binne shi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yayin da suke cikin gonar, matar Emmanuel ta gansu, ta gayyaci mijinta zuwa filin bisa zargin cewa wani yana kokarin binne laya a filin gidansu.

Bayanai sun nuna Emmanuel tare da matarsa ​​da danta da kuma surikinta suka far wa Joe da adduna, inda suka daɓa masa wuka a gonar.

Sai da suka yi wa Mista Joe dukan kawo wuƙa suka masa jina-jina, sannan suka ja shi zuwa gidansu da ke kusa da gonar, duk da matarsa da surukarsa sun sa baki.

Kara karanta wannan

Abun Tausayi: Mata da Miji da 'Ya'yansu Sun Mutu Sakamakon Wutar Lantarki Mai Ƙarfi a Jihar Arewa

Bayan an maida shi gida da kwanaki uku rai ya yi halinsa sakamakon jibgar da ya sha a hannunsu, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Kotu ta yanke musu hukuncin kisa

Alkalin kotun, Mai shari’a Winifred Effiong, ya samu ‘yan uwan biyu da laifin kisan kai kuma ya yanke musu hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Kotun ta bayyana cewa masu gabatar da kara daga ma’aikatar shari’a ta jihar sun tabbatar mata babu shakka cewa da gangan waɗanda ake zargi suka kashe Joe.

Kano: DSS Ta Kama Matar da Ta Yi Barazana Ga Shettima, Gawuna da Alkalai a Bidiyo

A wani rahoton na daban kuma Jami'an DSS sun cafke matashiyar nan da ta yi barazanar halaka Shettima, Gawuna da Alƙalan Ƙotun Kano kuma ta kashe kanta.

Fiddausi Ahmadu, 'yar kimanin shekara 23 a duniya ta yi wannan barazana ne a wani faifan bidiyo da ke yawo a soshiyal midiya.

Kara karanta wannan

Haɗarin Jirgi Ya Rutsa da Mutane Sama da 20 a Jihar Arewa, Ana Fargabar da Dama Sun Mutu

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262