Wakilin Jihar Kaduna Ya Fadi a Wajen Tantance Sababbin Ministocin Tinubu

Wakilin Jihar Kaduna Ya Fadi a Wajen Tantance Sababbin Ministocin Tinubu

  • An shiga cikin karamin rudani a majalisar dattawan Najeriya a lokacin da ake bakin aiki
  • A yau ne Sanatoci su ka shiga tantance wadanda ake sa ran za su zama sababbin ministoci
  • Sanatoci sun sa labule da Balarabe Abbas Lawal wanda zai wakilci Kaduna ya samu matsala

Abuja - Balarabe Abbas Lawal ya fadi kasa a yayin da ake tantance karin ministocin tarayya.

Malam Balarabe Abbas Lawal ya na cikin wadanda mai girma shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya gabatar da sunayensu.

A lokacin da sakataren gwamnatin na jihar Kaduna ya isa gaban ‘yan majalisa domin a tantance shi, sai aka ji ya fadi kasa.

Balarabe Tinubu
Balarabe Abbas Lawal ya fadi a majalisa Hoto: @officialasiwajubat
Asali: Twitter

Ana tantance karin Ministoci a Majalisa

Jaridar vanguard da ta kawo rahoton a yau Laraba, ba ta yi cikakken bayanin abin da ya faru ba, ana tunanin lamarin bai yi tsanani ba.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Majalisa Ta Fara Tantance Balarabe Da Sauran Mutane 2 Da Tinubu Zai Nada Minista

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ba abin mamaki ba ne gajiya ta jawo 'dan siyasa ya sume, an saba ganin irin haka.

Kafin nan, mun ji cewa Dr. Jamila Ibrahim Bio wanda ake so ta zama ministar matasa ta bayyana gaban 'yan majalisar kasar.

Balarabe Abbas Lawal ya fadi kasa

Tashar watsa labarai ta NTA ta kawo rahoto cewa abin da ya na faruwa sai Sanatocin su ka sa labule, aka dakatar da tantacewar.

Rahoto ya zo cewa shugaban majalisa, Godswill Akpabio ya bukaci ‘yan jarida su fice daga zauren bayan abin da ya faru kwatsam.

Abin ya faru ne yayin da wani Sanata yake jawabi a kan Lawal, a wani bidiyo da ke yawo, an ji Akpabio ya na cewa a nemo ruwa.

Sai bayan an kammala taron da shugabannin majalisa su ke yi za a bude zauren.

Kara karanta wannan

Sanatoci Sun Tsige Shugaban Majalisar Dattawa Daga Muƙaminsa Kan Abu 1? Gaskiya Ta Bayyana

Idan Balarabe Lawal ya tsallake matakin tantacewar, alamun sun tabbatar da shi ne zai zama sabon ministan muhallin tarayya.

Da zarar an tantance shi, wanda ya ragewa 'yan majalisar shi ne jagoran matasan jam'iyyar APC, Ayodele Olawande daga Ondo.

Wanene Balarabe Abbas Lawal?

Ku na da labari tun da Nasir El-Rufai ya zama ministan Abuja a 2003, yake tare da Balarabe Abbas Lawal, har ya sauka daga Gwamna.

Daga 2015 zuwa yanzu, Balarabe Abbas Lawal ya yi sakataren gwamnati sau uku a Kaduna, duk shi yake jagorantar shirin mika mulki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng