Jarumar Fina-finan Hausa, Hajia Binta Ola Ta Rasu A Jihar Katsina
- Masana'antar Kannywood ta shiga jimami bayan rasuwar daya daga cikin jarumanta a jiya Talata
- Marigayiya Hajiya Binta Ola ta rasu a daren jiya Talata 3 ga watan Oktoba a gidanta da ke jihar Katsina
- Shugaban hukumar tace fina-finai, Abba El-Mustapha shi ya bayyana haka da safiyar yau Laraba 4 ga watan Oktoba a shafinsa na Facebook
Jihar Katsina - Jarumar fina-finan Kannywood mai suna Hajiya Binta Ola ta riga mu gidan gaskiya a Sabuwar Unguwa Kofar Kaura da ke Katsina.
Shugaban Hukumar ta ce fina-finai, Abba El-Mustapha shi ya bayyana haka da safiyar yau Laraba 4 ga watan Oktoba a shafinsa na Facebook.
Yaushe jarumar Kannywood, Binta Ola ta rasu?
Ya ce za a yi sallar jana'izarta yau Laraba da misalin karfe 10 na safe a gidanta dake Sabuwar Unguwa Kofar Kaura a Katsina.
Kungiyar NLC Ta Fadi Yawan Mafi Karancin Albashi Da Za Su Tattauna Da Gwamnati, Ta Yi Wa Ma'aikata Albishir
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Marigayiya Binta Ola ta rasu ne a daren jiya Talata 3 ga watan Oktoba a jihar Katsina, TRT Afirka Hausa ta tattaro.
Rahotanni sun tabbatar cewa Binta Ola ta gama shirya yin bikin Maulidi kenan a yau Laraba kamar yadda ta saba ashe ba za ta ga wannan rana ba.
An tabbatar da cewa marigayiyar ta saba gudanar da Maulidi a ko wace shekara kamar yadda ta shirya yi a yau Laraba 4 ga watan Oktoba.
Meye mutane ke cewa kan jaruma Binta Ola?
Jarumar ta yi fice musamman a shirin 'Dadin Kowa' mai dogon zango na tashar Arewa24 da kuma wasu fina-finan Hausa.
Ta yi fina-finai da dama yayin da ta ke kan kaifinta a masana'antar ta Kannywood masu fadakar da jama'a.
Masu jimami da dama sun bayyana marigayiyar a matsayin mai hakuri da kuma iya zama da mutane.
Mahaifiyar Young Sheikh ta riga mu gidan gaskiya
A wani labarin, ana cikin jimami yayin da mahaifiyar Dakta Zakeer wanda aka fi sani da Young Sheikh ta rasu.
Mijin marigayiyar shi bayyana haka a shafinsa na Facebook inda ya yi addu'ar ubangiji ya mata rahama.
Young Sheikh ya kasance mai karancin shekaru da ke wa'azi a fadin Najeriya wanda jama'a da dama ke ganin ya yi kankanta.
Asali: Legit.ng