VC Na Udus Ya Yi Karin Haske Kan Harin Yan Bindiga a Jami'ar
- Farfesa Lawal Bilbis, mataimakin shugaban jami'ar Usmanu Dan Fodio (UDUS), ya yi ƙarin haske kan rahoton cewa ƴan bindiga sun kai hari makarantar a ranar Lahadi
- A wani taron manema labarai a ranar Talata, Farfesa Bilbis ya bayyana cewa abin da ya faru harin ƴan fashi ne saɓanin abin da ake yayatawa a shafukan sada zumunta
- Daga nan sai Bilbis ya yi kira ga iyaye da al'ummar jami’ar da su kwantar da hankalinsu, inda ya ƙara da cewa babu wani abin damuwa dangane da batun tsaron ɗaliban makarantar
Jihar Sokoto - Hukumar gudanarwar jami'ar Usmanu DanFodiyo da ke jihar Sokoto ta musanta rahoton cewa wasu ƴan bindiga sun kai hari a harabar jami’ar a ranar Lahadi, 1 ga watan Oktoba.
A wata sanarwa da ta fitar domin yin ƙarin haske kan lamarin a ranar Talata, 3 ga watan Oktoba, mahukuntan jami’ar sun ce harin na ƴan fashi ne ba na ƴan bindiga ba kamar yadda ake yayatawa, cewar rahoton Leadership.
VC na DUS VC ya yi ƙarin haske kan rahoton harin da ƴan bindiga
Farfesa Lawal Bilbis, mataimakin shugaban jami'ar, a wani taron manema labarai a ofishinsa, ya ce jita-jitar ta saɓa wa abin da ya faru, inda ya ce ƴan bindiga ba su kai hari a jami'ar ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Daga nan sai Farfesa Bilbis ya yi kira ga al'ummar jami'ar da iyayen yara da su kwantar da hankalinsu, inda ya ƙara da cewa babu wani abin fargaba game da tsaron rayukan ɗaliban makarantar.
Mataimakin shugaban jami'ar ya miƙa godiyar sa ga ƴan jarida bisa yadda suka tantance lamarin, inda ya ƙara da cewa hakan zai daƙile fargabar da ake ta yaɗawa a shafukan sada zumunta.
Yadda ƴan fashi da makami suka kaiwa UDUS hari
Ya ce jami’an tsaro na jami’ar ne suka sanar da shi lamarin, kuma sai da ya ziyarci inda aka kai harin da misalin ƙarfe 11 na daren wannan rana.
Bilbis ya bayyana cewa daga abin da idanuwansa suka gane masa, abin da ya faru a wajen fashi ne, ba harin ƴan bindiga ba.
A kalamansa:
"Sun ɗauki kwali biyu na Maltina da wayoyi takwas na ɗalibai waɗanda suke cajinsu a wasu shagunan da ke wajen."
Daliban OAU Sun Kulle Kofar Jami'ar
A wani labarin kuma, ɗaliban jami'ar Obafemi Awolowo da ke Ile-Ife a jihar Osun, sun fusata kan ƙarin kuɗin makarantar da mahukuntan jami'ar suka yi.
Ɗaliban sun yi dafifi inda suka kulle babbar ƙofar shiga jami'ar suna neman sai an rage kuɗin makarantar da kaso 50%.
Asali: Legit.ng