Tinubu Ya Zabi Sabbin Ministoci 3, Ya Tura Sunansu Majalisa Don Tantancewa

Tinubu Ya Zabi Sabbin Ministoci 3, Ya Tura Sunansu Majalisa Don Tantancewa

  • Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya aike da sunayen sabbin ministoci uku ga majalisar dattawa domin tantancewa
  • Sabbin ministocin sun haɗa da Jamila Bio (jihar Kwara), Balarabe Abbas (jihar Kaduna) da Olawale Olawande (jihar Ondo)
  • Jamila Bio za ta zama ministar matasa yayin da Olawale Olawande zai zama ƙaramin ministan matasa

FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya aike da wasiƙa zuwa ga Majalisar Dattawa domin neman amincewarta kan ƙarin ministoci guda uku.

Jaridar NTA News ta rahoto cewa shugaban ƙasar ya aike da wasiƙar wacce ta ƙunshi sunayen sabbin ministocin guda uku, a ranar Talata, 3 ga watan Oktoban 2023.

Shugaba Tinubu ya aike da sunayen sabbin ministoci
Shugaba Tinubu ya nemi majalisar ta amince da su Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Sabbin ministocin dai su ne, Dr. Jamila Bio, Balarebe Abbas da Olawale Olawande.

Su waye sabbin ministocin Tinubu?

Balarabe Abbas shine wanda Tinubu ya zabo daga jihar Kaduna don maye gurbin tsohon gwamnan jihar Nasir El-Rufai wanda aka gaza tantance shi saboda dalilai na tsaro.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Ɗumi: 'Yan Bindiga Sun Kai Farmaki Jami'ar Usman Ɗanfodiyo Da Ke Jihar Sakkwato

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar Sahara Reporters, a ranar 17 ga watan Satumba, Tinubu ya amince da nadin Dr. Jamila Bio Ibrahim daga jihar Kwara a matsayin ministar matasa, har zuwa lokacin da majalisar dattawa ta tabbatar da ita.

Shugaban ƙasar ya ƙara amincewa da naɗin Olawale Olawande daga jihar Ondo, domin ya zama ƙaramin ministan matasa.

Mai ba shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkokin watsa labarai labarai Ajuri Ngelale ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa.

Sanarwar ta bayyana Dakta Jamila Bio Ibrahim a matsayin "matashiyar likita" wacce a baya-bayan nan ta riƙe muƙamin shugabar ƙungiyar ‘Progressive Young Women Forum’ (PYWF).

Sanarwar ta kuma tattaro cewa Dokta Jamila ta yi aiki a matsayin babbar mataimakiya ta musamman ga gwamnan jihar Kwara kan manufofin SDGs.

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

"Shugaban ƙasa ya ƙara amincewa da naɗin Ayodele Olawande a matsayin karamin ministan matasa, har sai majalisar dattawa ta amince da shi."

Kara karanta wannan

Karin Albashin N35k Da Jerin Tallafin Da Shugaba Tinubu Ya Fito Da Su Bayan Cire Tallafin Man Fetur

Shi ma ministan wanda ya fito daga jihar Ondo, Mista Yewande, ya taba rike muƙamin shugaban matasa a jam'iyyar All Progressives Congress (APC), kuma ƙwararre ne wajen cigaban al'umma.

Tinubu Ya Sauyawa Ministoci Ma'aikatu

A wani labarin kuma, shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sauyawa wasu daga cikin ministocinsa ma'aikatu.

Abubakar Momoh ya tashi daga ma'aikatar matasa zuwa ma'aikatar cigaban yankin Niger-Delta. Adegboyega Oyetola ya bar ma'aikatar sufuri zuwa ma'aikatar kula da arziƙin teku.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng