Mutane 30 Sun Nutse Cikin Ruwa Bayan Jirginsu Ya Kife a Jihar Kebbi

Mutane 30 Sun Nutse Cikin Ruwa Bayan Jirginsu Ya Kife a Jihar Kebbi

  • An samu aukuwar wani mummunan hatsarin jirgin ruwa wanda ya ritaa da sama da mutum 50 a jihar Kebbi
  • Hatsarin jirgin ruwan ya auku ne bayan kwale-kwalen ya kife cikin kogi a ƙaramar hukumar Yauri ta jihar
  • Hukumomi na cigaba da ganin an ciro gawarwakin mutanen da lamarin ya ritsa da su domin yi musu jana'iza

Jihar Kebbi - Aƙalla mutane 30 ne suka nutse a ruwa yayin da kwale-kwalen da ke dauke da fasinjoji sama da 50 ya kife a ƙaramar hukumar Yauri ta jihar Kebbi a ranar Litinin.

Jaridar The Punch ta tattaro cewa shugaban ƙaramar hukumar Yauri, Bala Yauri ya tabbatar wa gidan rediyon Muryar Amurka wannan mummunan hatsarin ta wayar tarho, inda ya ce lamarin ya jefa al'ummar ƙaramar hukumar cikin baƙin ciki.

Kara karanta wannan

Haɗarin Jirgi Ya Rutsa da Mutane Sama da 20 a Jihar Arewa, Ana Fargabar da Dama Sun Mutu

Jirgin ruwa ya yi hatsari a jihar Kebbi
Mutum 30 suka nutse a hatsarin jirgin Hoto: Vanguard.com
Asali: UGC

Ya ce ana ci gaba da ƙoƙarin gano gawarwakin fasinjojin da suka nutse a cikin kogin, rahoton TVC News ya tabbatar.

Yadda hatsarin ya auku

A kalamansa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"A bayanan da na tattara, sama da mutum 50 ne hatsarin ya rutsa da su yayin da wasu daga cikinsu suka tsira amma zuwa yanzu da nake magana da ku sama da mutum 30 daga cikinsu sun maƙale a cikin kogin."
"Mun tattaro mutanen da suka iya ruwa a yankin domin gwada gano gawarwakin wadanda abin ya shafa domin ciro su da yi musu jana'iza kamar yadda addinin musulunci ya tanada."
"Kwale-kwalen kamar yadda na ji ya dauko fasinjoji ne waɗanda galibinsu ƴan kasuwa ne daga Jihar Neja ko Jihar Kebbi tare da kayan abinci da za a sayar kafin aukuwar lamarin."

Menene ya haddasa aukuwar hatsarin?

Kara karanta wannan

Dole za ku sha wahala: Tinubu ya ce 'yan Najeriya su shirya shan kebura, gyara babu dadi

Shima da yake nasa jawabin, wani da ya shaida lamarin, Alhaji Sani Yauri, ya tabbatar da cewa hatsarin ya auku ne sakamakon iska mai karfin gaske wacce ta sanya direban ya kasa tuƙa jirgin.

"Ina a wajen lokacin da lamarin ya auku, hatsarin ya auku ne a sakamakon iska mai ƙarfin gaske wacce ta sanya direban jirgin ya rasa yadda zai yi, inda nan take ya kife." A cewarsa

A halin da ake ciki, ba a samu jin ta bakin kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kebbi, DSP Nafiu Abubakar ba, saboda bai ɗauki kiran da aka yi masa ta waya ba, kuma bai dawo da saƙonnin da aka tura masa ba, har ya zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton.

Kwale-Kwale Ya Kife Da Fasinjoji a Adamawa

A wani labarin kuma, an sake samun wani hatsarin jirgin ruwa a jihar Adamawa, a ƙauyen Gurin cikin ƙaramar hukumar Fufore.

Hatsarin wanda ya ritsa da fasinjoji waɗanda galibinsu mata ne da ƙananan yara, ya auku ne a ranar Litinin, 11 ga watan Satumban 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng