Farashin Gas Mai Nauyin Kilo 12 Ya Kai N12,000, Zai Iya Kai Wa N18,000 Zuwa Disamba
- Farashin iskar gas mai nauyin kilo 12 ya tashi daga kasa da dubu 10 zuwa Naira dubu 12,500 a cikin 'yan makwanni
- Kungiyar dillalan iskar gas din sun bayyana cewa dalilin bai wuce tashin Dala da ake samu a kasar baki daya
- Dillalan su ka ce farashin iskar din mai nauyin kilo 12 na iya kai wa Naira dubu 18 zuwa watan Disamba idan ba a dauki mataki ba
Yayin da komai ke kara tashi a Najeriya, farashin iskar gas kullum kara sama ya ke saboda wasu dalilai.
Idan har ba a dauki wani mataki ba, farashin gas mai nauyin kilo 12 na iya kai wa Naira dubu 18.
Nawa ake siyar da iskar gas din a Najeriya?
Wannan na zuwa yayin da farashin ya tashi daga kasa da dubu 10 zuwa Naira dubu 12,500.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Legit ta tattaro cewa 'yan kasuwa sun kara farashin daga kasa da dubu 10 a watan Satumba zuwa dubu 12,500.
Shugaban kungiyar dillalan iskar gas a Najeriya, Olatubosun Oladapo ya yi gargadin cewa farashin gas mai nauyin kilo 12 na ya kai wa dubu 18 zuwa watan Disamba.
Wane hasashe aka yi kan farashin gas?
Ya ce hakan zai iya faruwa idan har gwamnati ba ta dauki wani kwakkwaran mataki ba aka haka.
'Yan Najeriya na biyan Naira dubu daya a ko wane kilo daya wanda a watannin baya kadan su ke biyan Naira 600 zuwa 700.
Oladapo ya ce duk ganawar da su ke ta yi da gwamnatin dole ta dauki matakan dakile hauhawan farashin kayayyaki.
Ya ce 'yan kasuwar na siyan tan 20 na gas akan kudi Naira miliyan 14 a ma'ajiyar mai din, VON ta tattaro.
N1000 Kowace KG: Yan Najeriya Sun Koka Kan Karin Farashin Gas Yayin da Kasar Ke Bikin Cika Shekaru 63
Ya kara da cewa a yanzu su na kashe Naira miliyan 1.7 don jigilar gas daga Legas zuwa Arewacin Najeriya saboda tsadar bakin mai.
'Yan Najeriya sun koka kan farashin iskar gas
A wani labarin, Mutane da dama sun nuna damuwa kan yadda farashin iskar gas na girki ke kara tashi a kasar.
Wannan na zuwa ne yayin da farashin ya kai Naira dubu daya ko wane kilo inda jama'a ke kokawa bayan irin wahalhalun da ake ciki.
Dillalan iskar gas a Najeriya sun yi hasashen farashin na iya ninkuwa idan gwamnati ba ta dauki mataki ba.
Asali: Legit.ng