Kotun Amurka Ta Umarci Jami’ar Chicago Ta Saki Shaidar Karatun Tinubu a Jami’ar
- Atiku ya samu dama a Amurka, inda kotu ta amince a nuna masa takardun shaidar karatun shugaba Tinubu a Jami'ar Jihar Chicago
- Atiku ya bayyana zargin ba lallai Tinubu ya yi karatu a jami'ar ta Amurka ba, ya fadi hakan a gaban kotun kararrakin zabe
- Ko ta yaya samun takardun zai taimaki Atiku, wannan lamari ne da zai bayyana bayan ganin shaidar karatun
Illinois, Amurka - Kotun yanki a jihar Illinois ta Amurka ta umurci Jami’ar Jihar Chicago da ta saki takardun shaidar karatun Shugaba Bola Tinubu, The Cable ta ruwaito.
A wata takardar da mai shari'a Nancy Maldonado ta bayar, kotun ta yi fatali da karar da Tinubu ya yi na hana tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar samun damar ganin takardun.
Idan baku manta ba, Atiku, wanda dan takarar jam’iyyar PDP ne a zaben shugaban kasa na 2023, ya shigar na neman a sake dukkan bayanan tarihin zaman Tinubu a jami'ar ta Amurka.
Sai dai, an kai ruwa rana sosai a kotu, inda a farko wata kotu ta hana a ba da takardun ko kuma nuna su ga dan takarar jam'iyyar adawar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda batun yake
A baya, an bayyana zargin ko dai shugaban kasar bai yi karatu a jami'ar ba kamar yadda ya yi ikrari, lamarin da ke kara kawo shakku a siyasar kasar nan.
Ba sabon abu bane a Najeriya a zargi shugaban kasa ko wani dan siyasa da nade lauje tare da ikrarin yin karatu a jami'a.
Wannan ne yasa dan takarar shugaban kasa a PDP ya maka Tinubu a kotu tare da kalubalantar tabbacin yin karatunsa a Jami'ar Jihar Chicago.
Atiku ya samu nasara a kotu
A baya kunji yadda aka bayyana nasarar Atiku a kotun game da karar da ya shigar da kuma yadda aka kaya.
An ba Atiku damar ganin takardun Tinubu da tarihin zamansa a jami'ar har ya kammala digiri na farko, kamar yadda rahotanni suka bayyana a baya.
Wannan zai zama babban lamari ga dan takarar na shugaban kasa a jam'iyyar PDP kasancewar ya dogara da samun wata hujja daga takardun.
Asali: Legit.ng