Muna Kara Kaimi Wajen Kawo Matakan Rage Wahalhalun Da ’Yan Najeriya Ke Ciki, in Ji Tinubu
- Shugaban kasa Tinubu ya ce yana kokarin tabbatar da an samu mafita ga matsalolin da ake fuskanta a kasar baki daya
- Ya ce, yana aiki don tabbatar da an dawo daidai yayin da kasar ke fuskantar karyewar farashin kudi da tsadar kayayyaki
- Tinubu ya kuma yi bayanin yadda zai kawo karshen matsalar tsaro ta hanyar amfani da dabarun zamani
Kaduna - Shugaba Bola Tinubu ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa gwamnatinsa na kara zage damtse wajen kawo matakan da za su kawar da mawuyacin halin da 'yan kasar ke ciki sakamakon cire tallafin man fetur da lalacewar darajar Naira.
Tinubu ya ba da wannan tabbacin ne a lokacin da yake jawabi a bikin faretin yaye sojiji da aka gidanar Kwalejin Tsaro ta Najeriya da ke Kaduna, The Nation ta ruwaito.
Shugaban wanda ya samu wakilcin mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima, ya ce hakazalika zai yi aiki wajen tabbatar magance talauci da ayyukan ta’addanci a dukkan kasar.
Shugaban ya kuma jaddada kudirin gwamnatinsa na kawar da talauci, ta’addanci da duk wani nau’in aikata laifi a Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abubuwan da Tinubu ke son yi
A wani bangare na yunkurin magance bangarorin ayyukan 'yan ta'adda, Shugaba Tinubu ya bayyana cewa gwamnatinsa ta fara kawo sabbin dabarun tsaro na zamani don magance matsalar tsaron kasar.
A cewarsa, tunkurin na sa zai kai ga magance matsalolin tsaro a Najeriya baki da ma sauran kasashen nahiyar Afrika.
Najeriya da sauran kasashen Afrika ta Yamma na yawan fama da ayyukan ta'addanci da 'yan tada kayar baya, musannan bayan samun tsaiko da aka yi a kasar Libya tare da hambarar da mulkin Gaddafi a baya.
Tinubu zai yiwa 'yan kasa jawabi gobe Lahadi
A bangare guda, rahoton da ke fitowa daga fadar shugaban kasa ya bayyana cewa, shugaba Bola Ahmed Tinubu zai fitowa ya yiwa 'yan Najeriya jawabi, TheCable ta ruwaito.
Zai yi jawabi ga 'yan kasar nan ne a ranar Lahadi 1 ga watan Oktoba a daidai lokacin fara bikin murnar cika shekaru 63 da samun 'yancin Najeriya.
Wannan na fitowa ne daga wata sanarwar da mai ba Tinubu shawari kan harkokin yada labarai, Ajuri Ngelale a ranar Asabar.
Asali: Legit.ng