Yan Sanda Sun Cafke Masu Garkuwa Da Mutane Mutum 4 a Benue
- Rundunar ƴan sandan jihar Benue ta samu nasarar yin caraf da wasu mutum huɗu da ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne
- Jami'an rundunar ne daii suka cafke miyagun bayan sun yi bata kashi da su a ƙauyen Agbanor na jihar
- Jami'an ƴan sandan sun kuma ceto wasu mata huɗu da miyagun suka sace lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa gona
Jihar Benue - Rundunar ƴan sandan jihar Benue ta cafke wasu mutum huɗu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne tare da kuɓutar da mutum shida daga maɓoyarsu a ƙauyen Agbanor da ke ƙaramar hukumar Okpokwu ta jihar Benue.
Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, Catherine Anene, ta ce an cafke waɗanda ake zargin ne bayan ƴan sanda sun ƙaddamar da farautar kuɓutar da wasu mata shida da aka sace a hanyarsu ta zuwa gona a ƙaramar hukumar Ado ta jihar.
Anene a cikin wata sanarwa ta bayyana sunayen wadanda ake zargin su huɗu waɗanda suka haɗa da Muhammed Ibrahim, Usman Sule, Azoto Alhaji da Abubakar Shehu, cewar rahoton Daily Trust.
A ina aka cafke miyagun?
A kalamanta:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"A ranar 22/9/2023 da misalin ƙarfe 5:00 na safe, ƴan sanda na Ado sun sun samu labarin cewa an yi garkuwa da ƴan mata huɗu da mata biyu a lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa gona a gundumar Utonkon. A yayin gudanar da bincike, ƴan sanda tare da hadin gwiwar wasu jami’an tsaro sun bi sawu tare da kai farmaki a maboyarsu a kauyen Agbanor da ke ƙaramar hukumar Okpokwu."
"Lokacin da suka yi ido huɗu da ƴan sandan, ɗaya daga cikin wadanda ake zargin ya yi musayar wuta da jami'an tsaron amma sun yi masa taron dangi inda suka cafke shi tare da ƙwace bindiga guda ɗaya dauke da harsasai. An kuma cafke sauran mutum ukun da ake zargi a yankin."
Anene ta ƙara da cewa mutum shidan da aka ceto sun samu kulawa a asibiti kuma an miƙa su zuwa ga iyalansu, inda ta bayyana cewa har yanzu a na cigaba da gudanar da bincike domin cafke sauran waɗanda ake zargin.
Yan Bindiga Sun Sace Mata Da Yayanta
A wani labarin kuma, ƴan bindiga sun yi awon gaba da wata mata tare da ƴaƴanta guda uku a ƙauyen Ajilete na jihar Kwara.
Miyagun ƴan bindigan sun dira a ƙauyen ne inda suka riƙa harbi kan mai uwa da wabi ƙafin daga bisani su tasa ƙeyar mutanen zuwa cikin daji.
Asali: Legit.ng