Shettima Ya Jagorancin Taron NEC a Fadar Shugaban Kasa Da Ke Abuja
- Mataimakin shugaban ƙasa, Ƙashim Shettima, na jagorantar taron majalisar NEC yanzu haka a Aso Villa da ke Abuja
- Rahoto ya nuna gwamnonin jihohi da dama sun halarci taron na yau Alhamis karo na uku bayan rantsar da shugaban ƙasa, Bola Tinubu
- Wannam taro na zuwa ne kwanaki ƙalilan bayan kungiyoyin ma'aikatan Najeriya sun ayyana shiga yajin aikin sai baba ta gani daga 3 ga watan Oktoba
FCT Abuja - Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, na jagorantar taron majalisar ƙoli ta tattalin arzikin Najeriya (NEC) a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.
The Nation ta tattaro cewa yanzu haka Shettima na jan ragamar taron NEC na wannan watan kuma karo na uku tun bayan rantsar da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu.
Gwamnonin jihohin da suka halarci taron
Gwamnonin jihohin da aka hanga sun halarci taron sun haɗa da, Osun, Legas, Kaduna, Adamawa, Ribas, Benuwe, Sokoto, Delta, Ebonyi, Taraba, da kuma Nasarawa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Haka nan kuma Ministan babban birnin tarayya Abuja kuma tsohon gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya halarci taron da dai sauran mambobin NEC, kamar yadda daily trust ta ruwaito.
Wannan taro na yau Alhamis na zuwa ne kwanaki ƙalilan bayan ƙungiyoyin kwadago sun ayyana shirinsu na tsayar da harkoki cak gaba ɗaya ranar 3 ga watan Oktoba.
Ƙungiyoyin kwadagon sun ayyana shiga yajin aiƙin sai baba ta gani ne bisa abin da suka kira gazawar gwamnati na samar wa 'yan Najeriya mafita biyo bayan wahalhalun cire tallafin fetur.
A taron karshe ranar 17 ga watan Agusta, NEC ta amince da ware zunzurutun kudi har Naira biliyan 5 ga kowace jiha daga jihohi 36 da birnin tarayya Abuja.
Majalisa ta ɗauki matakin ne domin a siyo kayan abinci da takin zamani a wani bangare na kokarin rage radadin da aka shiga sakamakon cire tallafin man fetur a kasar nan.
Kotun Zaɓe Ta Yanke Hukuncin Kan Nasarar Wani Gwamma
A wani rahoton kuma An tabbatar da Fasto Umo Eno na jihar Akwa Ibom a matsayin sahihin wanda ya lashe zaɓen gwamna ranar 18 ga watan Maris, 2023.
Kotun zaɓe mai zama a Uyo, babban birnin jihar ta kori kararrakin jam'iyyun ADC da NNPP da 'yan takararsu bisa hujjar rashin cancanta.
Asali: Legit.ng