1 Ga Oktoba: Gwamnatin Kwara Ta Ce Ba Zata Yi Bikin Ranar Yancin Kai Ba
- Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq na jihar Kwara ya ce gwamnatinsa ba zata gudanar da shagalin ranar 'yancin kai ba
- Kwamishinar yaɗa labarai, MisisBola Olukoju, ce ta tabbatar da haka ranar Alhamis, ta ce an yi haka ne saboda yanayin da mutane ke ciki
- Ta yi kira ga ɗaukacin mazauna jihar Kwara da su yi amfani da hutun 1 ga watan Oktoba wajen yi wa jihar da Najeriya baki ɗaya addu'a
Jihar Kwara - Gwamnatin jihar Kwara ƙarƙashin shugabancin Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq ta ce ba zata gudanar shagulgulan ranar samun 'yancin kai ba.
Gwamnatin ta ce ba zata yi kowane irin biki na murnar zagayowar ranar da Najeriya ta samu 'yancin kai ba saboda yanayin da al'umma suka tsinci kansu, Tribune ta rahoto.
Kwamishinar yaɗa labarai ta jihar, Misis Bola Olukoju, ce ta tabbatar da haka a wata 'yar gajeruwar sanarwa da ta fitar ranar Alhamis, 28 ga watan Satumba, Leadership ta ruwaito.
A ranar Lahadi, 1 ga watan Oktoba, 2023 Najeriya zata cika shekaru 63 da samun 'yanci daga turawan mulkin mallaka, kuma bisa al'ada gwamnati kan shirya bukukuwan murna.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ba za a yi kowane shagali ba ranar 1 ga watan Oktoba a jihar Kwara
A sanarwan da ta fitar, kwamishinar yaɗa labarai, Misis Olukoji ta ce:
"Mun ɗauki wannan matakin ne bisa la'akari da halin da mutane ƙasa ke ciki a daidai lokacin da ake kan gyare-gyare da kuma yunkurin gwamnati na tabbatar da ci gaba mai ɗorewa."
"Gwamnatin jihar mu ta buƙaci mutane da su yi amfani da hutun ranar 1 ga Oktoba wajen yi wa jiharmu da kasarmu da ma duniya gaba daya addu'a."
A halin da ake ciki Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar 2 ga watan Oktoba, 2023 a matsayin ranar hutu domin murnar zagayowar ranar da Najeriya ta samu 'yancin kanta.
Ebonyi: Jam'iyyar PDP Zata Daukaka Kara Kan Hukuncin Kotun Zaben Gwamna
A wani labarin kuma Jam'iyyar PDP ta kudiri aniyar ɗaukaka ƙara kan hukuncin Kotun zaɓe na tabbatar da nasarar gwamnan jihar Ebonyi.
A cewarsa PDP, ba ta gamsu da hukuncin ba musamman kan batun sauya sheƙa da zama mamban jam'iyyar APC.
Asali: Legit.ng