Yan Ta'addan Boko Haram Sun Halaka Mutum 4 a Jihar Borno
- Ƴan ta'addan Boko Haram sun kai sabon hari a jihar Borno inda suka salwantar da rayukan mutum uku
- Ƴan ta'addan sun halaka mutanen ne ciki har da jami'in soja a wani harin kwanton ɓauna da suka kai musu a kan titin hanyar Gwoza-Limankara
- Mutane da dama ne kuma ƴan ta'addan na Boko Haram suka yi awon gaba da su a harin tare da ƙona motoci masu yawa
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Borno - Ƴan ta'addan Boko Haram sun halaka mutum huɗu ciki har da soja ɗaya a wani harin kwanton ɓauna da suka kai musu a kan titin hanyar Gwoza Limankara mai nisan kilomita 134 talatin daga birnin Maiduguri.
An halaka mutanen ne a wani ayarin motocin da suka haɗa da ƴan sakai na CJTF da sojoji waɗanda ke raka fasinjoji a kan hanyar, cewar rahoton Channels tv.
Tashin Hankali Yayin da 'Yan Bindiga Suka Yi Garkuwa da Babban Malami da Wasu 2 a Babban Birnin Jihar APC
Hakazalika ƴan ta'addan na Boko Haram sun yi awon gaba da mutane da dama yayin da suka ƙona wata motar sintiri ta sojoji da wasu motoci guda biyar, rahoton Leadership ya tabbatar.
Yadda lamarin ya auku
Wata majiya mai tushe ta bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 5:00 na yammacin ranar Asabar, 23 ga watan Satumba, amma rashin hanyar sadarwa ta sanya lamarin bai bayyana ba har sai ranar Lahadi da yamma.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Majiyar ta bayyyana cewa:
"Ina sanar da ku cewa kimanin fararen hula uku da soja ɗaya ne aka kashe a wani harin kwanton ɓauna da ƴan Boko Haram suka yi musu a kan hanyar Gwoza-Limankara-Uvaha."
"Sojan yana daga cikin jami'an tsaro da ke aikin raka masu ababen hawa da fasinjoji akan wannan hanya."
"Kusan motocin sufuri guda biyar da wata motar sintiri ta jami'an sojoji ne aka cinnawa wuta. Har ya zuwa yammacin ranar Lahadi akwai mutane da dama waɗanda ba a san inda suke ba a cikin dajin."
Sai dai, har ya zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton, hukumomin soji ba su ce komai ba dangane da harin na ƴan ta'addan Boko Haram.
Jami'an Tsaro Sun Dakile Harin Yan Ta'adda
A wani labarin kuma, jami'an tsaro sun samu nasarar daƙile harin wasu ƴan bindiga da suka zo satar mutane a jihar Katsina.
Jami'an tsaro sun yi musayar wuta da ƴan bindigan, inda daga ƙarshe suka samu nasarar fatattakarsu.
Asali: Legit.ng