Ministan Shari'a Fagbemi Ya Bayyana Dalilin Da Ya Sa Ya Yarda Ya Zama Ministan Tinubu
- Antoni Janar kuma ministan shari’a, Lateef Fagbemi, ya ce shi bai yi kamun ƙafa ba domin zama minista a majalisar ministocin Shugaba Bola Tinubu
- Fagbemi ya ce ya amince ya yi aiki a gwamnatin shugaba Tinubu ne domin ya ba da gudummawarsa wajen cigaban Najeriya
- Ministan shari’ar ya ƙara da cewa ba shi da CV har zuwa lokacin da aka zabe shi saboda bai taba neman muƙamin ba
Ado-Ekiti, Jihar Ekiti - Antoni Janar kuma kuma ministan Shari’a, Lateef Fagbemi ya bayyana dalilin da ya sa ya amince ya yi aiki a gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
A cewar rahoton Nigerian Tribune, Fagbemi ya ce ya yi mamaki lokacin da aka zaɓe shi a matsayin wanda za a ba muƙamin minista.
Dalilin da ya sa na yarda na zama ministan shari’a na Tinubu, Fagbemi
Babban lauyan ya ce ya amince da naɗin da Shugaba Tinubu ya yi masa a matsayin minista ne saboda yana son bayar da irin ta sa gudunmawar domin cigaban Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya bayyana haka ne a lokacin da ya ke jawabi a wajen wata liyafa da mambobin 'Emmanuel Chambers' ƙarkashin jagorancin Aare Afe Babalola, SAN suka shirya a Ado-Ekiti, jihar Ekiti a ƙarshen mako.
Ban yi kamun ƙafa domin zama ministan Tinubu ba
Fabgbemi ya bayyana cewa bai yi kamun ƙafa ba domin a naɗa shi minista, wanda hakan ya sanya ya yi mamaki da naɗin da aka yi masa.
Ya yi kira ga ƙwararru da masu fasaha da su shiga a dama da su kada su bar sha'anin mulki a hannun ƴan siyasa kawai.
A kalamansa:
"Ban gabatar da wata takarda ko kamun ƙafa ba domin a naɗa ni minista. Na san mutane da yawa sun yi ta maganganu amma zan iya cewa ban san komai ba game da nadin minista. Shugaban ƙasa ya gaya min, "Kada ka yarda kowa ya yaudare ka, ina son ka shi ya sa na naɗa ka."
"Maganar gaskiya ita ce bani da CV har zuwa lokacin da aka zaɓe ni saboda ban buƙatarsa a rayuwata. Lokacin da na isa hukumar DSS, sun yi mamakin bani da haɗaɗɗen CV."
Gwamna Yahaya Bello Ya Bayyana Burinsa Barin Mulki
A wani labarin kuma, gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi ya bayyana babban burinsa bayan ya bar mulkin jihar.
Gwamnan ya bayyana cewa burinsa shi ne ya taimaka wa Shugaba Tinubu ya yi nasara a mulkinsa, domin nasararsa ta ƴan Najeriya ce gaba ɗaya.
Asali: Legit.ng