Babbar Magana Ta Taso Yayin da Lauya Ya Nemi Kotu Ta Garkame Wasu Ministocin Tinubu Kan Wani Batu

Babbar Magana Ta Taso Yayin da Lauya Ya Nemi Kotu Ta Garkame Wasu Ministocin Tinubu Kan Wani Batu

  • Wani lauya, Daniel Makolo, ya bukaci kotun masana’antu ta kasa da ke Abuja da ta tasa keyar ministocin shugaban kasa Bola Tinubu biyu magarkama
  • Olubunmi Tunj-Ojo da Lateef Fagbemi, ministan harkokin cikin gida da babban lauyan gwamnatin tarayya kuma ministan shari'a, sune ministocin biyu da abin ya shafa
  • Makolo ya shaida wa kotun cewa ministocin da wasu shugabannin hukumomi a kasar sun ki bin umarnin kotu na a mayar da shi aiki a hukumar shige da fice ta Najeriya a matsayin Kwanturola

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, AbujaLauya Daniel Makolo, ya shigar da kara a gaban kotun masana’antu ta kasa da ke Abuja, inda ya bukaci a daure wasu ministocin shugaban kasa Bola Tinubu saboda rashin bin umarin kotu a hukuncinta na ranar 4 ga watan Janairun 2023.

Kara karanta wannan

Labari Mai Daɗi: TUC Ta Bayyana Abinda Ministan Tinubu Ya Faɗa Mata Kan Batun Ƙarin Albashi

Kamar yadda jaridar Punch ya ruwaito, ministocin da ake magana a kai sun hada da Olubunmi Tunj-Ojo da Lateef Fagbemi.

Tunji-Ojo ne ministan harkokin cikin gida yayin da Fagbemi kuma shi ne babban lauyan gwamnatin tarayya kuma ministan shari'a.

An nemi a garkame ministocin Tinubu
Shugaba Tinubu na Najeriya a cikin hotuna | Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Baya ga ministoci, akwai wasu

Sauran wadanda aka maka a kotun sun hada da hukumomin Hukumar Tsaro ta Civil Defence, Ma'aikatan Gidan Yari da kuma Shige da Fice da Kashe Gobara.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A 2017, an kori Makolo daga hukumar shige da fice ba bisa ka'ida ba, kamar yadda ya bayyanawa kotu a karar da ya shigar.

Ya kuma bukaci kotun da ta garkame Wura Adepoju, mukaddashin Kwanturolan Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa da Folashade Yemi-Esan, Shugabar Ma’aikata bisa rashin bin umarnin kotun na dawo dashi aiki.

Lauya ya kawo jerin ministocin Tinubu da ya nema a daure

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Dattawan Kasar Yarabawa Sun Tubewa Obasanjo Rawanin Sarautar Balogun Na Owu Da Wasu Sarautun

A farkon watan Janairu ne kotun ta umurci ministan harkokin cikin gida da shugaban ma’aikata da masu ruwa da tsaki da su mai da Makolo bakin aiki tare da ba shi mukamin kwanturola, amma ministan ya yi watsi da umarnin kotun.

An kai ruwa rana game kan lamarin a gaban kotu, inda a yanzu aka sanya ranar 9 ga watan Oktoba don ci gaba da sauraran batun da ya sake shigarwa.

An bukaci wadanda ake kara da su bayyana a gaban kotu, su kuma bayyana dalilin da ya sa ba za su bi umarnin da aka basu ba.

Tinubu ya dakatar da wani batu ta hannun minista

A wani labarin, Tinubu ya ba da umarnin dakatar da batun ba sallama filin jirgin saman da kamfanin sufurin jirgin Najeriya

A cewar shugaban kasar, na daga cikin manyan ayyukan da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi a kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.