Oyo: Shugabar Matan APC Ta Riga Mu Gidan Gaskiya, Sanata Ya Yi Ta'aziyya
- Allah ya yi wa shugabar matan jam'iyyar APC ta mazaɓar jihar Oyo ta arewa, Princess Adebowale Atoyebi rasuwa
- Sanatan Oyo ta kudu, Sharafadeen Alli, ya yi ta'aziyyar wannan rashi ga iyalai da ɗaukacin mutanen jihar Oyo da APC
- Ya ce marigayyar ta kasance mace mai kamar maza da ke taimaka wa yan uwanta mata, kuma tana aiki tuƙuru
Jihar Oyo - Shugabar matan jam'iyyar APC ta shiyyar Oyo ta arewa, Princess Adebowale Atoyebi, ta riga mu gidan gaskiya ranar Alhamis, 21 ga watan Satumba, 2023.
Shugabar matan ta mutu ne shekaru ƙalilan bayan rasuwar mahaifinta Basarake, Alamodu na Ago-Amodu, Oba Lawal Oyetola Adebowale, kamar yadda The Nation ta ruwaito.
Sanatan Oyo ta kudu ya yi ta'aziyya
Sanata Sharafadeen Alli mai wakiltar mazaɓar Oyo ta kudu, ya bayyana rasuwar shugabar matan da babban rashi ga iyalanta da jam'iyyar APC baki ɗaya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanatan ya aike da saƙon ta'aziyya a wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Akeem Abas, ya fitar. Ya ce marigayyar shugaba ce mai kwazo, wacce ta yi aiki tuƙuru domin ci gaban jihar Oyo.
Wani sashin sanarwan ya ce:
"Cikin zuciya mai rauni mu ke samun labarin rasuwar Gimbiya Adebowale Adenike Atoyebi, shugabar mata ta jam’iyyar APC a mazaɓar Sanatan Oyo ta Arewa."
"Rasuwarta babban rashi ne ga jam’iyyarmu ta APC da kuma yanayin siyasar Najeriya baki ɗaya."
Ɗan majalisar dattawan ya ce Marigayya Atoyebi ta kasance mai taimakon mata a fagen siyasa, kuma zakara a yaƙi da wariyar launin fata da kuma abun alfaharin al’ummar Oyo ta Arewa.
Ya ƙara da cewa za a riƙa tunawa da Atoyebi saboda ta kasance jagora mai kishi kuma mai jajircewa kuma halayenta za su ci gaba da wanzuwa, Leadership ta rahoto.
Sanata Alli ya mika ta’aziyya ga iyalan marigayya Atoyebi, abokai da daukacin 'ya'yan jam’iyyar APC na jihar Oyo, inda ya yi addu’ar Allah ya ba su ikon jure wannan rashi mai raɗaɗi.
Ekiti: Abokin Takarar Segun Oni Ya Fice Daga SDP, Ya Koma Jam'iyyar APC
A wani rahoton na daban Jam'iyyar SDP reshen jihar Ekiti ta rasa ɗaya daga cikin manyan jiga-jiganta wanda ya tattara ya sauya sheƙa zuwa APC mai mulki.
Ladi Owolabi, abokin gamin Segun Oni, ɗan takarar gwamna a inuwar SDP a zaben da ya gabata, ya fice daga jam'iyyar zuwa APC.
Asali: Legit.ng